| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Ɗanwasan Sifaniya da ya ci Gasar Kofin Duniya Ferran Torres ya koma PSG daga Barcelona
Ƙungiyar ta Gasar Ligue 1 ta kashe dala miliyan 58 wajen siyan ɗan wasan mai shekara 26 kan yarjejeniyar shekara biyar.
Ɗanwasan Sifaniya da ya ci Gasar Kofin Duniya Ferran Torres ya koma PSG daga Barcelona
Torres na yazura wa Sifaniya ƙwallo a ragar Argentina a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya

Ɗan wasan tawagar Sifaniya Ferran Torres, wanda ya zura ƙwallo ɗaya tilo na wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2026, ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya da ƙungiyar Paris Saint-Germain daga ƙungiyar Barcelona.

Sai dai ƙungiyar ta kashe kudi dala miliyan 58  kafin ta samu ɗan wasan, in ji rahotanni.

“Paris Saint Germain tana farin cikin shelar cewa ta samu Ferran Torres. Ɗan wasan gaban Sifaniya da ya ci Gasar Kofin Duniya ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya da kulob ɗin zuwa shekarar 2031,” in ji wata sanarwa da kulob ɗin ta fitar ranar Asabar.

Torres ya bayyana a wata sanarwa cewa shi ya “ji daɗin cewa zai fara wata sabuwar tafiya a wata ƙungiya mai cike da buri irin Paris Saint Germain.”

“Za ni so na gode wa Shugaba Nasser Al-Khelaifi [mai bai wa PSG shawara] Luis Campos da koci Luis Enrique da damar da suka ba ni na komawa ƙungiyar, wadda nake fatan cewa zan taimaka wa wajen lashe kofi iya yadda za ta yiwu.”

Tsohon ɗan wasan Valencia da Machester City ɗin ya taɓa aiki da Luis Enrique wanda a matsayinsa na kocin Sifnaiya ya fara ba shi damar buga wa tawagar ƙasar a shekarar 2020 a wasan ƙasar da tawagar Jamus a Lig ɗin Ƙasashe.

Torres wand ya lashe gasar Laliga sau uku a Barceolona, ya shiga wasan ƙarshe a Gasar Kofin Duniya a matsayin wanda ya maye wani ɗan wasa kuma ƙwallon da ya zura a raga a cikin ƙarin lokaci ya hana Argentina kare kambinta.