An ayyana gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ta kudu maso yammacin Nijeriya da ƙuri'u 511,067. Ademola ya ci galaba kan 'yantakaran jam'iyyar APC da ADC ne yayin da ya zama gwamnan jihar a karo na biyu a jere
Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC ne ya zo na biyu a zaɓen inda ya sami ƙuri'u 444,815. Shi kuma Najeem Salaam na jma'iyyar ADC shi ne na uku da ƙuri'u 17,180 .
“Saboda haka, Adeleke Ademola Jackson na jam'iyyar Accord Party, bayan ya cika dukkan sharruɗan doka, ya zama wanda aka ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen,” kamar yadda babban jami'in zaɓen Joshua Ogunwole ya bayyana ranar Lahadi a cibiyar tattara ƙuri'u da ke Osogbo.
Ogunwole ya ce ƙuri'u 1,005,800 ne aka kaɗa a zaɓen, da aka yi a ƙananan hukumomi 30 na jihar Osun, yayin da aka ƙirga 985,079 masu inganci. Ya ce masu kaɗa kuri'u 1,010,684 ne aka tantance domin zaɓen.

















