| Hausa
WASANNI
4 minti karatu
Hukumomin ƙwallon ƙafa 6 na Larabawa, ciki har da Qatar da Morocco na goyon bayan Infantino na FIFA
Infantino, wanda ke neman a sake zaɓarsa a baɗi, ya fuskantar turjiya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyoyi uku — UEFA, AFC da CONCACAF — sun soki yadda yake tafiyar da harkokinsa tare da yin kira da ya yi murabus.
Hukumomin ƙwallon ƙafa 6 na Larabawa, ciki har da Qatar da Morocco na goyon bayan Infantino na FIFA
Shugaban FIFA Gianni Infantino / Reuters

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Larabawa guda shida, ciki har da Qatar da Morocco, wadda za ta karɓi baƙuncin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2030 tare da wasu ƙasashe, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaban FIFA Gianni Infantino a ranar Alhamis, yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafar duniya ke fuskantar rikici sakamakon gazawar wani shirin neman jarin kamfanoni masu zaman kansu.

Infantino, wanda ke neman a sake zaɓensa a baɓi, ya fuskanci turjiya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyoyi uku — UEFA, AFC da CONCACAF — sun soki yadda yake tafiyar da harkokinsa tare da yin kira da ya yi murabus saboda wani shiri da ya gaza, na jawo jarin kamfanoni masu zaman kansu cikin wasannin FIFA, ciki har da Gasar Cin Kofin Duniya.

Shugaban na FIFA ɗan ƙasar Switzerland ya gabatar da shirin ware haƙƙin kasuwanci na gasar tare da sayar da kashi 20 cikin 100 ga masu zuba jari masu zaman kansu domin tara kusan dala biliyan 4.2, kafin daga bisani ya janye shirin sakamakon matsin lamba da ya biyo baya.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, shugabannin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa shida sun ce: “Bisa la’akari da muhimmiyar rawar da ƙwallon ƙafar Larabawa ke takawa wajen haɗa kan mutane da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a faɗin ƙasashen Larabawa, muna bayyana cikakken goyon bayanmu ga Mista Gianni Infantino, shugaban FIFA, tare da sake tabbatar da amincewarmu da jagorancinsa da kuma ci gaba da ƙoƙarinsa na bunƙasa ƙwallon ƙafa a duniya.”

Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, ne ya sanya hannu kan sanarwar, tare da Hany Abo Rida, shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Masar, da shugabannin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Lebanon, Morocco, Sudan da Mauritania.

Hudu daga cikin waɗanda suka rattaba hannu — Al Thani, Abo Rida, Fouzi Lekjaa na Morocco da Ahmed Yahya na Mauritania — su ma mambobi ne na Majalisar FIFA.

Sun ce suna matuƙar jin daɗin ƙoƙarin Infantino na ci gaba da bunƙasa ƙwallon ƙafa a duniya, faɗaɗa damammaki a dukkan yankuna da kuma ƙarfafa rawar da ƙwallon ƙafa ke takawa wajen haɗa kan mutane da al’ummomi.

Sun ƙara da cewa suna fatan ci gaba da aiki kafada da kafada da shi domin samar da makoma mai ƙarfi da wadata ga ƙwallon ƙafa ta duniya, tare da faɗaɗa damammaki da kuma ƙara ƙarfafa gudunmawar ƙwallon ƙafar Larabawa ga wasan ƙwallon ƙafa na duniya.

Ireland ta janye goyon bayanta

A ranar Alhamis kuma, Ireland ta shiga jerin ƙasashen da suka janye goyon bayansu ga Infantino.

Hukumar Kwallon Ƙafa ta Ireland ta ce bayan wani taron kwamitin gudanarwarta, an yanke shawarar janye wasiƙar goyon bayan da ta aika a farkon shekarar, sannan ta sanar da FIFA dalilan matakin.

Ta ce tana godiya da irin tallafin da FIFA ke bai wa ƙwallon ƙafar Ireland, amma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun haifar da damuwa sosai kan kyakkyawan shugabanci, gaskiya da kuma rashin cikakkiyar tuntuba.

Shirin Infantino da aka janye ya zo da tallafin dala miliyan 20 ga kowace ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa a zagaye na gaba na tallafin FIFA. Adadin zai iya ninkawa idan ƙungiyoyin suka amince da yarjejeniyar.

Bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a Morocco a makon da ya gabata, FIFA ta nemi afuwa daga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mambobi 211 bisa kura-kuran da aka samu wajen gudanar da shirin, tare da cewa shugabannin FIFA suna da cikakken goyon bayan Infantino.

Duk da adawar ƙungiyoyin nahiyoyi uku da ke wakiltar ƙasashe mambobi 136 daga cikin 211 da za su kada kuri’a a zaɓen shugaban FIFA a watan Maris, Infantino har yanzu yana da dimbin magoya baya a harkar ƙwallon ƙafa.

Goyon bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa shida, waɗanda da yawa daga cikinsu mambobi ne na AFC, ya nuna cewa ba zai yiwu a samu zaɓen ƙuri’a gaba ɗaya bisa ƙungiyoyin nahiyoyi ba, domin kowace ƙasa mamba tana da ƙuri’a guda.

Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ita ma ta bayyana goyon bayanta ga Infantino.

Idan Infantino zai fafata da ɗan takara guda ɗaya kacal, zai buƙaci samun rinjaye na ƙuri’u 106 domin samun nasara a zaɓen shekara mai zuwa.

Sai dai idan ’yan takara uku ko fiye suka tsaya, Infantino zai buƙaci samun kashi biyu bisa uku na ƙuri’u, wato ƙuri’u 141, a zagayen farko na zaɓen.