| Hausa
AFIRKA
4 minti karatu
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Ecuador na cikin mutum 7 da suka mutu a hatsarin helikwafta a Kenya
Shugaban hukumar sirri ta Ecuador, Michele Sensi-Contugi, da matarsa, Stephany Hollihan Vasconez, suna cikin mutane bakwai da suka mutu a cikin wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Kenya a ranar Laraba, kamar yadda gwamnatin Ecuador ta sanar.
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Ecuador na cikin mutum 7 da suka mutu a hatsarin helikwafta a Kenya
Shugaban hukumar leken asirin Ecuador Michele Sensi-Contugi da matarsa sun mutu a wani hatsarin helikofta a Kenya a ranar 19 ga watan Agusta, 2026.

Shugaban Hukumar Leƙen Asiri na Ecuador Michele Sensi-Contugi da matarsa, Stephany Hollihan Vasconez, suna cikin mutane bakwai da suka mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Kenya ranar Laraba, in ji gwamnatin Ecuador.

"A yau Michele da Stephany sun bar mu da wuri. Hankulanmu na tare da iyalansu, musamman 'ya'yansu da iyayensu," in ji Ministan Sufuri na Ecuador Roberto Luque a X.

Hatsarin ya faru ne a Tsaunin Ololokwe a gundumar Samburu, kimanin kilomita 270 arewa da babban birnin Kenya, Nairobi.

Biyar daga cikin sauran mamatan Amurkawa ne, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.

Mutanen suna tsaka da yawon shaƙatawa ne a lokacin da jirgin ya faɗi, kuma ba a fayyace sanadin hatsarin ba tukuna.

Fitaccen ɗankasuwa

Michele Sensi-Contugi, mai shekaru 44, fitaccen ɗan kasuwar Ecuador ne kuma shugaban Centro de Inteligencia Estratégica (CIES), Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa ta Ecuador.

Harkokin kasuwancinsa sun haɗa da sufurin jiragen sama na yawon buɗe ido da na yawon shaƙatawa, haka nan kuma yana samar da kayan robobi.

An haife Sensi-Contugi ne a Desio, a lardin Monza-Brianza na Italiya, cikin wani iyali mai tarihi a Tuskan, a ranar 12 ga Agusta, 1982. Mahaifinsa ɗan Italiya ne, mahaifiyarsa kuma 'yar Ecuador.

Ya yi suna a sassan masana'antu da kasuwanci na Ecuador kafin ya riƙe manyan muƙamai na gwamnati.

Harkokinsa na siyasa sun shahara a 2024 a ƙarƙashin Shugaba Daniel Noboa, lokacin da ya riƙe muƙamin ministan gwamnati tsakanin Afrilu da Agusta na 2024 kafin a naɗa shi matsayin Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Centro de Inteligencia Estratégica (CIES).

Kariya ta gwamnati

Yana da shaidar zama ɗan ƙasa biyu, Italiya da Ecuador, Sensi-Contugi ya zama fitacce a harkokin kasuwanci da siyasa a Ecuador. Naɗinsa a matsayin shugaban hukumar leken asiri ya sanya shi cikin wadanda ke kula da ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin gwamnati masu muhimmanci kuma na sirri.

Matarsa, Stephany Hollihan Vasconez, wadda ita ma ta mutu a hatsarin na helikwafta, fitacciyar mai zanen kaya ce kuma tsohuwar mai tallar kayan ƙawa a Ecuador, har ta zama sananniya a masana'antar tufafi ta ƙasar.

Lokacin da ya riƙe shugabancin hukumar ta CIES ya zo ne a lokacin da gwamnatin Noboa ta sanya tsaro na ƙasa da leken asiri a gaba cikin ƙoƙarinta wajen magance ƙaruwar matsalar tsaro a Ecuador.

An kaddamar da bincike

Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Kenya (KCAA) ta tabbatar da mutuwar mutane a hatsarin na ranar Laraba, tana mai cewa tana mika "ta'aziyya" ga iyalan mamatan bayan wannan al'amari mai ban tausayi.

Ma'aikatar kula da sufurin jiragen sama ta bayyana cewa jirgin da hatsarin ya shafa nau'in Eurocopter EC130 B4 ne, mai lambar rijista 5Y-GYM. Ta ce Jirgin ya tashi ne daga Loisaba zuwa Ewaso Nyiro lokacin da ya faɗi da misalin ƙarfe 9:13 na safe agogon yankin a Dutsen Ololokwe.

KCAA ta ƙara da cewa tana yin aiki tare da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don bincike kan hatsarin.

Sashen Binciken Hadarin Jiragen Sama na Ma'aikatar Sufuri ta Kenya ne ke jagorantar binciken yanayin da ya janyo faɗuwar jirgin. Hukumar ba ta bayyana abin da zai iya zama sanadin hatsarin ba.

Masu yawon buɗe ido suna yawan amfani da helikwafta

Yankin da ke kewaye da Dutsen Ololokwe, wanda ake kira Ol Donyo Sabache, yanki ne na yawon bude ido a arewacin Kenya, wanda ke jan hankalin baƙi daga ƙasashen waje zuwa gandun dajin dabbobi a faɗin yankin.

Ana amfani da ƙananan jiragen helikwafta sosai wajen jigilar masu yawon buɗe ido, tsakanin wuraren yawon buɗe ido gandun daji, a sassa masu nisa na arewacin Kenya.

A cewar KCAA, masu bincike na aiki don gano abin da ya haifar da wannan hatsari.