Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jaddada matsayinsa kan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi, yana mai cewa kiran da ɗaya daga cikin masu adawa da shi ya yi na a dawo da tallafin, “alamar babban rashin sanin yadda gwamnati da tattalin arziki ke aiki ne.”
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis lokacin da ya karɓi Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Ƙasa, sai dai bai bayyana sunan wanda yake nufi ba.
Martanin Tinubu ya zo ne kwana guda bayan tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi wata hira inda ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
“To, mu duba yadda tarihi ya nuna mana abubuwa. Na ga ɗaya daga cikin masu adawa da ni yanzu yana cewa zai dawo da tallafi.
“Na karanta hakan. Wannan alama ce ta babban rashin sanin yadda gwamnati da tattalin arziki ke aiki,” in ji shi.
Shugaban ƙasar ya ce kafin ya hau mulki a shekarar 2023, gwamnatocin jihohi 27 ba su iya sauke nauyin da ke wuyansu na biyan ma’aikata albashi, kuma suna dogaro da gwamnatin tarayya.

“Kafin na zo nan, jihohi 27 ba su iya biyan albashi, balle ma a yi maganar fansho da albashin ma’aikata.
“A jiharka ma, na san wani mutum da ake wa laƙabi da ‘Half Salary’. Suna zuwa wajen gwamnatin tarayya suna roƙo, ba su iya yin komai. Albashin da kuke biya yana ciyar da iyalai,” in ji shi.
“Suna a ƙananan hukumomi. Suna cikin jihohi. Ina ne mafi yawan jama’a suke? Suna cikin jihohi.
“A cire Shugaban Ƙasa daga wannan batu. A ɗauki kowa a matsayin talaka mai iyalin da yake ciyarwa.
“Ababen more rayuwa da kuke aiwatarwa kamar hanyoyi, gidaje, gyaran makarantu, asibitoci, shirye-shiryen kiwon lafiya, farfaɗo da harkar lafiya, horas da malamai da kuma horar da ma’aikatan lafiya domin kare iyalanmu masu rauni, duk suna daga cikin nauyin da ke kanku,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur ne a lokacin jawabinsa na rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Duk da sukar da ya sha daga ’yan Nijeriya da shugabannin adawa, waɗanda suka koka kan tashin farashin man fetur, abinci da sauran abubuwa, Shugaban Ƙasar ya ce matakin da ya ɗauka yana da amfani ga tattalin arzikin ƙasa da kuma ’yan ƙasa.


















