| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Ayyukan ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila na barazana ga ƙoƙarin zaman lafiya a Ƙudus: Turkiyya
"Ankara za ta ci gaba da kare haƙƙin al'ummar Falasɗinu da na birnin Kudus a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa," in ji Shugaban hukumar Sadarwa na Turkiyya.
Ayyukan ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila na barazana ga ƙoƙarin zaman lafiya a Ƙudus: Turkiyya
Shugaban Hukumar Sadarwa Burhanettin Duran ya yi gargaɗi game da ayyukan gwamnatin Netanyahu da ke barazana ga matsayin Kudus.

Shugaban Sashen Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, ya yi Allah wadai da "kakkausar murya" kan harin da Isra'ila ta kai a Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Ƙudus da aka mamaye wanda ministan tsaron ƙasar ya jagoranta.

"Ina Allah wadai da harin da wani Ministan Majalisar Ministocin Isra'ila ya jagoranta, tare da rakiyar wata tawagar masu tsattsauran ra'ayi, kan Masallacin Ƙudus. Ba za a yarda da duk wani yunƙuri na kai hari kan wuri mai tsarki na Masallacin Ƙudus ba," kamar yanda Duran ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Alhamis.

"Irin waɗannan hare-hare na kisan ƙare-dangi da gwamnatin (Benjamin) Netanyahu ke yi da nufin lalata matsayin tarihi da na shari'a kan Birnin Ƙudus na ƙara ta'azzara tashin hankali a yankin da kuma fatan dakushe ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa," in ji shi yana mai gargaɗi..

Yana mai jaddada kalaman shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kan kare matsayin tarihi na Birnin Ƙudus da masallacin Ƙudus, Duran ya ce ba wai kawai nauyin da ya rataya a yanki ne ba kawai, har da nauyin da ke kan al'ummomin duniya na kare waɗannan wurare.

Ya yi alƙawarin cewa Ankara za ta ci gaba da kare haƙƙin al'ummar Falasɗinu da na Birnin Kudus ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Ƙarkashin umarnin Ministan Tsaron Ƙasa na Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi, Itamar Ben-Gvir ne, kimanin 'yan kama-wuri-zauna na Isra'ila 1,300 ne suka afkawa harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Gabashin birnin Kudus da aka mamaye a ranar Alhamis, suna bikin ranar Yahudawa ta Tisha B'Av, suna tunawa da abin da suka kira "rusa wurin ibadan," a cewar Hukumar Birnin Kudus.