Rundunar Sojin Nijeriya ta ayyana ɗaya daga cikin jami'anta a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin sayar wa 'yanta'adda da sauran masu aikata laifuka kayan sojoji ba bisa ƙa'ida ba, tana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin cafke shi domin ya fuskanci hukunci.
A cikin wata sanarwa da Sashen kula da makamai da kayayyakin aikin soja na sojin ƙasa na Nijeriya ya fitar, sunan sojan da ake nema Farabiti Mohammed Yusuf Amutu, wanda ke aiki a sashen ɗinka inifam na sojin ƙasa na Nijeriya kafin ya tsere daga sansaninsa a ranar 3 ga Yunin 2026.
Rundunar ta ce binciken farko ya danganta sojan da sayar da kayan na soji da kuma kai su ga 'yanta'adda da sauran masu aikata laifuka ba tare da izini ba, lamarin da ya sa hukumomin soji suka ayyana shi a matsayin wanda ake nema.
Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma ƙoƙarin gano inda yake domin cafke shi, inda idan aka kama shi zai fuskanci cikakken bincike da matakan ladabtarwa da suka dace bisa dokokin soja.
Rundunar Sojin Nijeriya ta jaddada cewa ba ta lamuntar duk wani nau'in rashin ɗa'a, karya doka ko wani aiki da zai iya kawo rauni game da aikinta, mutuncinta da martabarta, ko kuma ya zama barazana ga tsaron ƙasa.
Ta yi gargaɗin cewa duk wani jami'in soja da aka samu da laifin taimaka wa 'yanta'adda, masu aikata laifuka ko wasu ƙungiyoyi ta hanyar sayarwa, karkatarwa ko rarraba kayan soji ba bisa ƙai’da ba zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa dokokin soja da na farar-hula.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama'a da su ba da sahihan bayanan da za su taimaka wajen cafke sojan da ake nema, tana mai roƙon duk wanda ke da wani bayani da ya kai shi ga ofishin soja mafi kusa ko kuma kowace hukuma ta tsaro.
Sashen kula da makamai da kayayyakin aikin soja na sojin ƙasa na Nijeriya ya sake tabbatar da jajircewarta wajen tabbatar da gaskiya, ƙwarewa da kare kadarorin soji, tana mai cewa za ta ci gaba da ƙarfafa matakan sa ido na cikin gida tare da tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike kan duk wani zargin rashin ɗa'a, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da ya dace.















