| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Sifaniya ta zama ƙasa ta farko da ta riƙe Kofin Duniya na maza da na mata, da kofin nahiya a tare
Nasarar Sifaniya ta sa ƙasar ta kafa tarihi da dama, ciki har da kasancewar kocin tawagar mai shekaru 65, Luis de la Fuente, mafi tsufa da ya jagorancin zakarun gasar Kofin Duniya.
Sifaniya ta zama ƙasa ta farko da ta riƙe Kofin Duniya na maza da na mata, da kofin nahiya a tare
Wannan ne karo na biyu da Sifaniya ta lashe Kofin Duniya bayan wanda ta lashe a 2010 a Afirka ta Kudu.

Ƙasar Sifaniya ta kafa tarihin zama ƙasa ta farko a tarihin ƙwallon ƙafa da ta samu nasarar riƙe Kofin Duniya na maza da na mata a lokaci guda, wanda FIFA ke shiryawa.

Wannan ya tabbata ne bayan da ƙasar ta yi nasarar lashe Kofin Duniya na maza ranar Lahadi, 19 ga Yulin 2026 a birnin New York na Amurka, a gasar da ta gudana a Amurka, Canada, da Mexico.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ce ta tabbatar da wannan sabon tarihi bayan da Sifaniya ta zama zakarar gasar FIFA 2026. Da ma Sifaniyan ce ke riƙe da Kofin Duniya na FIFA na mata wanda ta lashe a Australia a 2023.

Bugu da kari, Sifaniya ce ke riƙe da babban kofin gasar ƙasashen nahiyar Turai na Euro, wanda ta lashe a 2024, kuma ba za a sake buga gasar ba sai a 2028.

Nasarar Sifaniya ta sa ƙasar ta kafa tarihi da dama, ciki har da kasancewar kocin tawagar mai shekaru 65, Luis de la Fuente, mafi tsufan kocin da ya jagorancin zakarun gasar Kofin Duniya.

A wasan ƙarshe na gasar FIFA 2026, sai da aka kai zagayen ƙarin lokaci kafin Sifaniya ta ci ƙwallo guda ta hannun Ferran Torres, a wasan da Argentina ta ƙare da ‘yanwasa 10.

A minti na 93 ne alƙalin wasa ya sallami Enzo Fernendez bayan ba shi yalon kati na biyu, wanda ya koma jan kati.

Wasan dai ya kasance na ɓangare guda saboda Argentina ta gaza kai farmaki kan raga a tsawon minti 115 na farkon wasan. Sai a mintunan ƙarshe ne suka yi yunƙurin tagazawa ba tare da nasara ba.