Fiye da mutane 40 ne aka yi garkuwa da su bayan wasu 'yanta’adda sun kai jerin hare-hare a wasu al'ummomi da ke Jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda mazauna yankin da mahukuntan ƙaramar hukuma suka bayyana.
A cewar wani mazaunin gundumar Mayanchi da ke ƙaramar hukumar Maru, 'yanta’addan sun kai hare-hare a ƙauyuka 11 tsakanin ranar Juma'a da Lahadi, inda suka kai farmaki al'ummomin Tashar Mayanchi, Gwargawo, Jidda da Garagi, da sauransu.
Mazaunin yankin, Alhaji Lauwali Abdullahi, ya ɗora alhakin harin kan wani gawurtaccen shugaban 'yanbindiga da aka fi sani da Kachalla Sa'idu, yana mai cewa an yi garkuwa da fiye da mutane 40 a hare-haren.
"Yanzu da nake magana da ku, fiye da mutum 40 daga cikin mutanenmu na hannun Kachalla," in ji Abdullahi.

Shugaban ƙaramar hukumar Maru, Bello Jabaka, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa ana ƙoƙarin neman ƙarin jami'an tsaro domin tura su yankunan da abin ya shafa.
"Ina aiki domin shigar da ƙorafi ta yadda za a turo mana da ƙarin jami'an tsaro zuwa yankin," in ji Jabaka.
Rundunar 'yansandan Jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
Ƙungiyoyin 'yanta’adda na ci gaba da addabar manyan yankuna a arewa maso yammaci da tsakiyar Nijeriya, inda suka shahara da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi, kai hare-hare kan ƙauyuka da kuma ƙaƙaba haraji ba bisa ƙa'ida ba kan manoma.
Ana kuma danganta su da ayyukan haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a yankin.
Wannan sabon harin na zuwa ne duk da ci gaba da hare-haren sojoji kan ƙungiyoyin 'yanta’adda a Zamfara.
A farkon wannan watan, mahukuntan jihar sun ce sojojin Nijeriya sun kashe fiye da 'yanta’adda 300 a cikin kwanaki biyu na gudanar da samame a jihar.

















