| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kashe gomman sojojin ƙasar Mali a harin kwanton-ɓauna
'Yan a-ware na ƙabilar Abzinawa a ƙasar Mali sun yi wa wani ayarin sojojin ƙasar kwanton-ɓauna a kusa da Anefis, kwanaki kaɗan bayan sojoji sun sake ƙwace garin na yankin arewa da ke da muhimmanci.
An kashe gomman sojojin ƙasar Mali a harin kwanton-ɓauna
'Yan a-ware na ƙabilar Abzinawa suna sintiru a wani tsohon barikin Africa Corps da ke Kidal, arewacin Mali

An yi wa wani ayarin sojojin Mali kwanton-ɓauna ranar Asabar da safe yayin da yake barin garin Anefis na arewacin ƙasar wanda ke da matuƙar muhimmanci, inda jami’an rundunar soji da ta tsaron ƙasar suka ce an kashe dakaru da dama.

A ranar 4 ga watan Yuli ne ‘yan a-aware na ƙabilar Abzinawa, JNIM, suka ƙwace garin na Anefis na wani ɗan lokaci, a wasu gagaruman hare-hare da suka ƙaddamar a sassan ƙasar.

"An kai wa tawagarmu hari da safiyar nan yayin da take barin Anefis a kan hanyar zuwa Gao a kusa da Tabankort. Ana ci gaba da gumurzu. An yi musu kwanton-ɓauna," a cewar wata majiya a Gao yayin hira da kamfanin dillacin labarai na AFP. Wata majiya daga FLA ta tabbatar da harin.

"A yi wa sojoji mummunar ɓarna, ko da yake sauran dakarun da ke ayarin sun ci gaba da tafiya," a cewar wani jami’in tsaro da ba ya so a ambaci sunansa, yayin da wani jami’in ya bayyana harin a matsayin wanda ya haddasa mummunar ɓarna.

A wasu hotuna da ƙungiyar FLA ta fitar ta bayyana cewa ta kama gomman sojojin Mali.

Gumurzun da aka yi a Anefis ranar 12 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar sojojin Mali kimanin 30 tare da jikkata kusan 60, a cewar wata sanarwa da ofishin babban hafsan sojin ƙasar ya fitar.

Kwana biyu kafin haka, sojojin Mali da rundunar sojojin-haya ta Rasha sun sake ƙwace garin bayan sun kwashe kwanaki da dama suna gwabza faɗa da ‘yan a-ware.