| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe mutane aƙalla 18 a Jihar Benue da ke tsakiyar Nijeriya, in ji mazauna yankin
'Yanbindiga sun kashe mutane aƙalla 18 a jihar Binuwe ta arewa matso tsakiyar Nijeriya a hare-haren da suka kai a ƙarshen makon jiya, kamar yadda mazauna yankin da jami'ai suka bayyana.
'Yanbindiga sun kashe mutane aƙalla 18 a Jihar Benue da ke tsakiyar Nijeriya, in ji mazauna yankin
'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 18 a jihar Benue da ke arewacin Najeriya a ranar 12 ga watan Yuli, 2026.

'Yanbindiga sun kashe mutane aƙalla 18 a jihar Binuwe ta arewa maso tsakiyar Nijeriya a harin da aka kai a ƙarshen mako, in ji mazauna da jami'an yankin.

Mai magana da yawun 'yansanda a Jihar, Udeme Edet, ya bayar da ƙididdiga mafi ƙaraanci ta adadin mutanen da suka mutu a harin da ya faru da safe a ranar Lahadi, yana cewa mutum takwas sun mutu sannan biyar sun ji raunuka.

Sai dai wasu jaridun Nijeriya sun ce adadin waɗanda aka kashe ya kai 18 a hare-haren da aka fara kaiwa tun ranar Juma’a.

Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne a al'ummar Otukpo-Nobi a ƙaramar hukumar Otukpo, inda mazauna suka ce wasu mutane ɗauke da makamai sun buɗe wuta tsakanin da misalin ƙarfe 3:30 da 4:30 na asuba.

Shugaban ƙaramar hukuma Maxwell Ogiri ya danganta tashin hankalin da aka gani da kisan shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani da aka yi makonni biyu da suka wuce.

Sai dai Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN reshen Jihar ta Binuwe ta nesanta kanta da kashe-kashen, sannan ta yi Allah wadai da hare-haren, kamar yadda ke ƙunshe a wata sanarwa da sakataren ƙungiyar Ibrahim Galma ya sanya wa hannu.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin.

Mata da matasa daga yankin da abin ya shafa sun yi zanga-zanga a garin Otukpo don nuna adawa da kisan.