An ceto tare da kuɓutar da dukan ɗalibai da malamai da aka sace yayin harin da aka kai wa al'ummar Ahoro-Esiele da ke Ƙaramar Hukumar Oriire a Jihar Oyo ranar 15 ga Mayu.
Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Kafafen Sada Zumunta, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a yammacin ranar Jumma'a.
An sace mutanen ne bayan wasu 'yanbindiga ɗauke da muggan makamai sun mamaye al'ummar, inda suka yi garkuwa da ɗalibai 46, malamai da kuma shugaban wata makarantar sakandare, lamarin da ya tayar da hankalin al'umma a faɗin ƙasar.
Lamarin ya ƙara muni kwanaki bayan sace mutanen, lokacin da masu garkuwar suka fille kan ɗaya daga cikin malaman da aka sace, Michael Oyedokun.
A yayin aikin ceto mutanen, jami'an tsaro sun kama 'yanbindiga takwas, waɗanda yanzu suke tsare a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (DSS), yayin da aka kashe wasu daga cikin masu garkuwar a yayin artabun.
Hukumomi sun ce ba a yi wata yarjejeniya ko musayar fursunoni domin ceto waɗanda aka sace ba.
Sun bayyana cewa ɗaya daga cikin fitattun jagororin masu garkuwar, wanda suka nemi a sake shi a matsayin sharadin sakin mutanen, na ci gaba da fuskantar shari'a kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
An kuma ce hukumomin tsaro za su fitar da cikakken bayani game da yadda aka gudanar da aikin ceto nan ba da jimawa ba.











