Hedkwatar rundunar “Operation Haɗin Kai” a Nijeriya ta ce wasu mutane shida da ake zargi mayakan ISWAP ne, tare da iyalansu, sun miƙa wuya ga dakarun bataliya ta 192.
Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Soji, na Hedkwatar Haɗin Gwiwa ta Shiyyar Arewa Maso Gabas (Operation Haɗin Kai) da ke Maiduguri, Kyaftin Mohammed Goni ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Laraba.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun bataliya ta 115, yayin da suke gudanar da ayyukan bincike da ceto a yankin ƙaramar hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno a ranar 7 ga watan Yuli, sun ceto ƙarin mutane biyu da aka sace a maɓoyar ’yanta’adda.
Ta ce za a ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da kuɓutar da mutane ba tare da gajiyawa ba, har sai an gano kowane mutum da aka sace kuma an mayar da shi ga iyalansa cikin ƙoshin lafiya.
Abubuwan da aka ƙwato a hannun ’yanta’addan da iyalansu sun haɗa da jimillar kuɗi sama da Naira miliyan 1.5, wayoyin salula na Tecno guda biyu, da sauran kayayyaki.
Haka kuma sojojin sun ce sun ƙwato ƙarin kuɗi Naira miliyan 1.2 da ake zargin na ayyukan laifuka ne, da kayan abinci, da sauran kayayyakin da ake zargi ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.

An kwashe mutanen da aka ceton zuwa wuri mai cikakken tsaro inda suke samun kulawar lafiya da ta ƙwaƙwalwa da ta dace.
A daidai wannan lokacin, dakarun sun bayyana cewa sun daƙile wasu hare-hare da mayaƙan ISWAP suka tsara kaiwa a Borno, inda aka kashe soja guda ɗaya.
“Ko da yake mayaƙan sun ɗan rusa wani ɓangare na katangar sansaninmu yayin musayar wuta mai zafi, dakarun sun yi hanzarin sake shiri, suka ƙaddamar da gagarumin harin ramuwar gayya, kuma sun fatattaki maharan gaba ɗaya, inda suka yi musu ɓarna mai yawa tare da tilasta wa ’yanta’addan da suka tsira gudu da raunin harbin bindiga daban-daban.”
“Abin takaici, soja guda ɗaya mai jajircewa ya rasa ransa, yayin da motocin yaƙi guda biyu da wasu kayan yaƙi suka lalace lokacin fafatawar.”
Sai dai kuma, sanarwar ta bayyana cewa a halin yanzu komai ya fara komawa daidai.
”FOB Logomani yana nan daram a ƙarƙashin ikon dakarun Operation HADIN KAI, inda aka tura ƙarin sojoji, ana ci gaba da bincike sannan ana aiwatar da ƙarin matakai don ƙarfafa kariyar wurin.”
Wasu nasarorin da aka samu na daban
A wata nasarar ta daban, dakarun bataliya ta 232 sun bayyana cewa sun kama wani gawurtaccen mai laifi a ƙaramar hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
Binciken da aka gudanar bayan kama shi ya kai ga ƙwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, albarusai guda biyu, da kuma harsasai na musamman guda 28 na 7.62mm.
Waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka ƙwato suna tsare a hannun sojoji, yayin da ake ci gaba da bincike don gano tare da kama sauran masu laifin.
Kazalika, sanarwar ta ce dakarun bataliya ta 149 sun kama mutane biyu da ake zargi da samar da kayayyaki ga ’yanta’adda a ƙaramar hukumar Mobbar ta Jihar Borno. Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da tsabar kuɗi, mota kirar Volkswagen Golf, kayan gini, kayan aikace-aikacen gida, da sauran kayayyakin da ake zargi an yi niyyar kai wa ‘yanta’adda. Ana gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin.
A wani ɓangare na hare-haren share-fage da ake ci gaba da yi, dakarun runduna ta 24 ta Task Force, tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai na “Civilian Joint Task Force” (CJTF), sun kai samame a wasu sanannun maɓoyun ’yanta’adda a kewayen Wulgo. Yayin aikin, sojojin sun gano wata jaka shaƙe da haramtattun ƙwayoyi daban-daban da ’yanta’adda da suka tsere suka bari.
Haka kuma, sojojin sun kama wani da ake zargi da samar da kayayyaki ga ƙungiyar BHT/ISWAP a shingen bincike na Molai, ɗauke da tarin magunguna masu yawa ba tare da izini ba. Shi ma yana tsare ana bincikensa.
Haka kuma, a yankin Sector 2, dakarun bataliya ta 233 Tank Battalion, tare da haɗin gwiwar wasu mafarauta, sun tare da kama wani da ake zargi da samar da kayayyaki ga BHT/ISWAP daga ƙauyen Ngirya na ƙaramar hukumar Tarmuwa, ɗauke da tayoyin babur guda biyar.
“Waɗannan nasarori na baya bayan nan suna nuna tasirin hare-haren da ake ci gaba da kaiwa, da sahihan bayanan sirri, da kuma kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da dakarun agaji wajen wargaza hanyoyin samar da kayayyaki ga ’yanta’adda, da daƙile ayyukan laifuka, da kuma kare al’ummomin da ke cikin hatsari a faɗin Arewa Maso Gabas,” in ji sanarwar.
Rundunar Operation Haɗin Kai ta jaddada gargaɗi mai tsauri ga ɗaiɗaikun mutane da ke da hannu wajen samar da abinci, mai, kayan gini, sufuri, ko kowane irin taimako ga ƙungiyoyin ta’addanci da su gaggauta daina yin hakan.
“Duk wanda aka samu yana taimakawa, ko haɗa baki da ’yanta’adda, ta kai-tsaye ko a kaikaice, za a gano shi, a kama shi, kuma a gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada,” in ji rundunar.











