| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin Sudan sun ƙwace ƙauyen Al-Kurmuk bayan arangama da dama da RSF
Al-Kurmuk yana da muhimmanci sosai wajen sarrafa hanyoyin safarar kayayyakin soji da hanyoyin da suka haɗa Ethiopia ko Habasha da Sudan ta Kudu.
Sojojin Sudan sun ƙwace ƙauyen Al-Kurmuk bayan arangama da dama da RSF
Sudan ta fada cikin rikici tun watan Afrilun 2023, lokacin da fada ya barke tsakanin dakarun sojin kasar da dakarun sa-kai na Rapid Support Forces. / AA

Dakarun sojin Sudan sun shiga garin Al-Kurmuk mai muhimmanci a gabashin Sudan a ranar Laraba bayan fafatawa da dama da dakarun sa-kai ta RSF, in ji majiyoyin soja ga Anadolu.

Majiyoyin, waɗanda suka yi magana bisa sharaɗin a ɓoye sunayensu, sun ce dakarun soja da ƙungiyoyin haɗin gwiwa sun shiga Al-Kurmuk bayan jerin ayyukan soja kan 'yan RSF da SPLM-N, inda suka sake kwace iko da garin.

Matakin ya biyo bayan nasarorin da sojin Sudan suka samu kwanan nan a jihar Blue Nile, inda suka sake ƙwato wurare da dama kusa da iyakokin Ethiopia da Kudancin Sudan, in ji majiyoyin.

Al-Kurmuk na ɗaya daga cikin manyan garuruwa a jihar Blue Nile, tare da birnin jihar, Ad-Damazin. Yana kusa da iyakar Habasha, kuma yana da muhimmanci ta fuskar dabaru saboda ta nan ne ake safarar kayan soji da hanyoyin mota da ke haɗa Sudan da Habasha da Kudancin Sudan.

A ranar 24 ga Maris ne RSF ta kwace iko da Al-Kurmuk.

Sudan ta kasance cikin rikici tun Afrilun 2023, lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin soja da RSF kan shirin shigar da rundunar RSF cikin rundunar sojin ƙasa.

Rikicin ya haifar da ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen jinƙai a duniya, inda ya janyo asarar dubban rayuka kuma ya tilasta wa kusan mutane miliyan 13 barin gidajensu.