| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Neymar ya yi bankwana da tawagar Brazil bayan Norway ta fitar da su daga Kofin Duniya
Tauraron ɗanwasan Brazil, Neymar Jr, ya sanar da yin ritaya daga tawagar ƙasarsa, bayan da Norway ta doke Brazil da ci 2-1 a wasan gasar Kofin Duniya na FIFA 2026.
Neymar ya yi bankwana da tawagar Brazil bayan Norway ta fitar da su daga Kofin Duniya
Neymar yana kuka bayan fitar bazata da Brazil ta yi daga Gasar Cin Kofin Duniya a hannun Norway. / Reuters

Neymar Jr, ɗanwasa mafi shahara cikin taurarin ƙwallon ƙafa daga Brazil a zamanin nan, ya sanar da yin ritaya daga buga wasa a tawagar ƙasa, bayan Brazil ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Norway.

Norway ta doke Brazil a zagayen ‘yan-16 na gasar Kofin Duniya na FIFA 2026, a wani wasa da aka buga a birnin Meadowlands na jihar New Jersey ta Amurka, a daren Lahadi 5 ga Yuli.

Brazil dai ƙasa ce da ta shahara a fagen ƙwallo, kuma ita ce ta fi kowa lashe gasar inda ta ɗaga kofin har sau biyar a tarihi.

An ga ɗanwasan mai shekaru 34 ya zube a ƙasa yana hawaye bayan an hura usur ɗin ƙare wasan, kafin abokan tawagarsa su zo su jajanta masa, inda kocin Brazil Carlo Ancelotti ya zo ya miƙa masa hannu don ya tashi.

Neymar ne ya zura ƙwallo guda da Brazil ta ci a wasan ta bugun fenareti ana minti na 10 na ƙarin lokaci, amma hakan bai ceto Brazil ba, inda ita kuwa Norway ta wuce matakin kwatafainal.

Filin wasan farko

Da yake jawabi cikin jimamai bayan wasan, Neymar ya ce, "Na yi ƙoƙari. Na yi ƙoƙari. Na fara wasa a wannan filin wasa na MetLife Stadium, kuma a nan nake ƙarewa. Yanzu dai komai ya ƙare".

Kalaman nasa na nuna cewa Neymar ya buga wasansa na farko a tawagar Brazil a filin wasan na MetLife ranar 9 ga Agustan 2010, a wasan sada zumunci tsakanin Brazil da Amurka.

Neymar ya yi ritaya ne a matsayin ɗanwasan da ya fi zura ƙwallaye ga Brazil, da ƙwallaye 80 a wasannin 130. Ya fara buga wa tawagar a 2010 bayan ya soma buga ƙwallon ƙwararru tare da Santos FC a 2009.

A 2016 Neymar ya ci lambar zinare tare da tawagar a gasar Olympics.

Ɗanwasan dai ya yi ta fama da ciwon ƙafa, wanda ya sa wasanni biyu kawai ya iya bugawa cikin biyar a gasar ta bana. A matakin rukuni, minti 15 kacal ya buga a wasansu da Scotland.

Neymar ya kasance mafi kyawun ɗanwasan Brazil cikin fiye da shekaru goma, duk da yawan jinya da ya yi ta fama da ita cikin shekaru, wanda ya taƙaita tasirinsa.