Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da zagaye na ƙarshe na shirinta na kwashe ‘yan ƙasar da suka maƙale a Afirka ta Kudu, tana mai gargaɗin cewa lamarin tsaro na cike da rashin tabbas inda babu alamar cewa hare-haren ƙin baƙi suna raguwa.
Gwamnatin ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da suke ganin cewa rayuwarsu na cikin haɗari su yi amfani da damar da ta yi saura ta tashin jiragen kuɓutar da ‘yan ƙasar, tana mai jaddada cewa ba za ta iya tabbaatar da tsaron waɗanda suka zaɓi ci gaba da zama a ƙasar ba a yanayin tashin hankalin da ake ciki .
Sabuwar shawarar na cikin wata sanarwar da aka wallafa a shafin Ministar Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya a X, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu.
Gargaɗi na baya bayan nan na zuwa ne kwanaki bayan gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan ‘yan Nijeriya biyu a Afirka Ta Kudu; Emeka Charles Iroegbu, wanda rahotanni suka ce jami’an ‘yan sandan Tshwane a birnin Pretoria ne suka kashe shi, da kuma Musa Yunana Joe, wanda aka fi sani da Big Joe, wanda aka kashe a gaban shagonsa a Witbank, Mpumalanga.
Gwamnatin ta nemi a yi cikakken bincike da kuma gurfanar da waɗanda suka aikata aika-aikar a gaban kotu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ministar ta ce Nijeriya ta damu matuƙa game da lafiyar ‘yan ƙasarta a Afirka ta Kudu yayin da hare-haren ƙin jinin baƙi ke ci gaba.
“Nijeriya ta damu matuƙa game da tsaron ‘yan ƙasarta a Afirka ta Kudu sakamakon zanga-zanga da hare-haren ƙin jinin baƙin da ake yi, bayan mutuwar ‘yan Nijeriya biyu, Musa Yunana Joe da Charles Iroegbu yayin lamarin na takaici,” in ji ta .
Ministar ta bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ta tsawaita kammala aikin kuɓutar da mutanen da aka tsara cewa zai ƙare ranar 30 ga watan Yuni sakamakon ci gaba da damuwa kan batun tsaro.
“Babu alamun cewa lamarin na ingantuwa,” kamar yadda ministar ta bayyana.
Ta yi kira ga ‘yan Nijeriya waɗanda har yanzu ba su yanke shawara ba game da komawa gida, su yi nazari a kan haɗɗuran a hankali, tana mai tuna musu cewa za a iya maye gurbin jari da aka rasa, amma ba za a iya maye gurbin rai ba.
“Ga mutane da yawa waɗanda har yanzu ba su yanke shawara ba , zai dace su san cewa kadarori da jari da aka rasa za a iya maye gurbinsu, amma wannan ba zai faru ga rayukan da aka rasa ba,” in ji ta.
Yayin da yake ba da ƙarin haske game da lokacin kuɓutarwar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya bayyana cewa wani jirgin kamfanin Air Peace zai bar Legas zuwa Johannesburg da misalin ƙarfe 3:30 na rana a ranar Talata 7 ga watan Yuli.










