| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Trump ya yabi Tinubu kan 'jagorancinsa a yaƙi da ta'addanci' a Nijeriya
A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yuli, 2026, Trump ya jinjina wa Tinubu bisa ƙudirinsa na magance matsalolin tsaro a Nijeriya, yana mai cewa Amurka na alfaharin tsayawa tare da Nijeriya a yaƙi da ta'addanci.
Trump ya yabi Tinubu kan 'jagorancinsa a yaƙi da ta'addanci' a Nijeriya
Tinubu da Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazo wajen yaƙi da ta'addanci da sauran matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yuli, 2026, Trump ya jinjina wa Tinubu bisa ƙudirinsa na magance matsalolin tsaro a Nijeriya, yana mai cewa Amurka na alfaharin tsayawa tare da Nijeriya a yaƙi da ta'addanci.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ne ya fitar da wasiƙar a ranar Laraba a shafinsa na X.

Trump ya ce, "Ina yaba wa ƙudirinka na magance matsalolin da ke addabar ƙasarka, musamman tashe-tashen hankulan da ke shafar al'ummomin Kiristoci.

Babbar ɗaukaka ce a gare ni mu kasance tare da kai a yaƙi da 'yanta'adda domin ganin Tarayyar Nijeriya ta zama ƙasa mafi ƙarfi da wadata."

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa dangantakar Amurka da Nijeriya na da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci da rikice-rikice ke ƙaruwa a Yammacin Afirka, yana mai cewa ƙasashen biyu suna da buri iri ɗaya na yaƙi da ta'addanci ta kowace fuska.

Ya kuma yi nuni da Taswirar Haɗin Gwiwar Tsaro ta Amurka da Nijeriya ta 2026 (US–Nigeria Defence Cooperation Roadmap), wadda ya ce ta samar da ingantaccen tsari na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

A cewarsa, Amurka ta tura dakarunta na musamman (US Special Operations Forces) domin horas da sojojin Nijeriya tare da ba su kayan aiki da bayanan sirri da za su taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da ta'addanci da kare rayuka.

Haɗin gwiwar tsaro tsakanin Abuja da Washington ya ƙara ƙarfi a cikin 'yan watannin nan.

A watan Nuwamban 2025, shugabannin ƙasashen biyu sun amince da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa, wanda masu ba shugabannin ƙasashen shawara kan harkokin tsaro ke jagoranta, domin bunƙasa musayar bayanan sirri, horaswa da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.

Mahukuntan Nijeriya sun ce ɗaya daga cikin sakamakon wannan haɗin gwiwar shi ne harin haɗin gwiwa da aka kai a 16 ga Mayu kan maɓoyar mayaƙan DAESH a yankin Tafkin Chadi, inda aka kashe jagoran ƙungiyar, Abubakar Al-Minoki, tare da wasu manyan kwamandojinsa.

Wannan ci gaba ya zo ne bayan ziyarar da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mai Kula da Afirka, Frank Garcia, ya kai Abuja a makon da ya gabata, inda ya yi alƙawarin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da sauran fannoni tsakanin Amurka da Nijeriya.