Shugaba Nijeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin a kama wani mutum mai suna Prince George Buchi Nwabueze nan take dangane da gano wani ofishi na bogi mai suna Ofishin Ayyuka na Musamman na Ƙasa, da aka yi.
Haka kuma shugaban na Nijeriya ya bayar da umarnin dakatar da wasu manyan sakatarori uku a ofishin sakataren gwamnatin ƙasar nan-take.
Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) Dokta Musa Adamu Aliyu, SAN ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ganawa da Shugaban Ƙasa a ranar Juma'a.
Manyan sakatarorin da aka dakatar su ne M.S Danjuma, da Injiniya Nadungu Gagare, da kuma Richard P. Pheelangwah.
Shugaban na ICPC ya ce an gano sabuwar hukumar ta bogi ne a wani ɓangare na binciken da ake yi kan Majalisar Tallafawa Harkokin Waje ta Shugaban Ƙasa ta bogi, wadda Adeyemi Matthew ke gudanarwa.
Ya ce an bai wa sabuwar hukumar da aka gano ta bogi ofishi ba bisa ƙa'ida ba a cikin harabar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.



















