| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Tsohon Ministan Tsaron Isra'ila Yaalon ya zargi Netanyahu da neman rikici da Turkiyya
Moshe Yaalon ya ce Netanyahu na rura wutar rikici da Turkiyya da gangan ta hanyar kai hari kan wani sansanin jiragen sama da ke arewacin Syria, inda ya zargi Firaministan da tsawaita rikice-rikice domin guje wa shari’a.
Tsohon Ministan Tsaron Isra'ila Yaalon ya zargi Netanyahu da neman rikici da Turkiyya
Yaalon ya ce Netanyahu ne ke da babban alhakin harin da kuma rikicin da Isra’ila ta shiga daga baya

Tsohon Ministan Tsaron Isra’ila, Moshe Yaalon, ranar Alhamis ya zargi Firaminista Benjamin Netanyahu da neman taƙalar faɗa da Turkiyya da gangan ta hanyar kai hari kan wani sansanin jiragen sama da ke arewacin Syria.

Yaalon ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa harin ya jawo Allah wadai daga Amurka.

Ya zargi Netanyahu da ci gaba da yaƙe-yaƙe a wurare daban-daban da kuma ƙoƙarin ƙaddamar da wasu domin kauce wa fuskantar shari’a kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba.

Yaalon ya ce Netanyahu ne ke da babban alhakin harin da kuma rikicin da Isra’ila ta shiga daga baya, yana mai iƙirarin cewa Firaministan na buƙatar yaƙin ya ci gaba domin hana kafa kwamitin binciken gwamnati kan abin da ya faru.

Bayan harin ranar 7 ga Oktoba, Netanyahu ya ɗauki ra’ayin wasu da Yaalon ya kira “masu akidar Almasihu”, kan cewa harin wani “abin al’ajabi” ne da za a iya amfani da shi wajen tayar da “yaƙin Gog da Magog,” in ji Yaalon.

Ya yi zargin cewa manufar ita ce mamaye abin da ake kira “Ƙasar Alkawari”, daga Kogin Euphrates a arewa zuwa “Ƙoramar Masar” a kudu, a kawar da waɗanda ba Yahudawa ba daga yankin sannan a zaunar da Yahudawa a wurin.

Game da Syria, Yaalon ya ce Isra’ila ta rasa wata dama bayan hare-haren da suka raunana Hezbollah da kuma kasancewar Iran a cikin ƙasar.

Dangane da Lebanon, Yaalon ya yi ikirarin cewa Shugaban Amurka Donald Trump na ƙoƙarin tilasta wa Netanyahu wata yarjejeniya da “za ta iya zama mai amfani ga Isra’ila,” amma Firaministan Isra’ila na ƙoƙarin guje mata.

Game da Iran, Yaalon ya ce Netanyahu ya nemi sauya gwamnati domin samun wata nasara da za ta rufe abin da ya bayyana a matsayin gazawar Firaministan.

Ya bayyana sakamakon a matsayin “wani wasan kwaikwayo na banza,” yana mai cewa hakan ya haifar da rikici tsakanin Netanyahu da Trump.

Yaalon ya kuma zargi Netanyahu da ƙoƙarin ƙara rura wutar rikici a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ta hanyar wasu mutane da ya bayyana a matsayin “masu kai hare-haren tarzoma,” waɗanda ya ce suna samun goyon baya da ƙarfafawa daga wasu ministocin gwamnatin Isra’ila.

Ya ce Netanyahu na yin watsi da abin da ya kira “jan kati” daga Jakadan Amurka Mike Huckabee, yana mai cewa hare-haren na ci gaba.

Yaalon ya ce harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Gabashin Kudus da aka mamaye na bai wa Netanyahu mafi kyakkyawar dama wajen rura wutar wani sabon yaƙi.

Ya yi kira ga shugabannin ’yan adawar Isra’ila da su mayar da hankalinsu wajen ƙoƙarin kawar da Netanyahu daga mulki domin ceton rayukan fararen-hula da sojoji tare da “hana ƙarin barna.”