Hukumar Tsaro ta NSCDC a Nijeriya ta tsare kwamandanta na Jihar Neja da aka dakatar, Suberu Aniviye da wasu jami'an hukumar da ake alaƙanta su da mutuwar mutum 37 da ake zargi masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba ne.
Jami'an sun bayyana a hedkwatar NSCDC ta ƙasa da ke Abuja a ranar Lahadi, yayin da kakakin hukumar na ƙasa, ACC Babawale Afolabi, ya yi wa manema labarai ƙarin haske kan sakamakon binciken farko da hukumar ta gudanar game da lamarin.
Ya ce an dakatar da wasu ƙarin ma'aikata uku dangane da wannan mummunan lamari, baya ga waɗanda aka riga aka bayyana sunayensu a baya.
Haka kuma Afolabi ya bayyana cewa, wani aikin haɗin gwiwa da Rundunar Bincike ta Musamman (SIS) ta Babban Kwamandan Hukumar ta gudanar, ya kai ga sanya dukkan jami'an rundunar ta Jihar Neja da ke da hannu a wannan mummunan aiki a ƙarƙashin sanya ido na musamman a hedkwatar hukumar ta ƙasa
Kazalika Babban Kwamandan hukumar na ƙasa Farfesa Ahmed Abubakar Audi ya bayar da umarnin a sauke tutar NSCDC ƙasa-ƙasa a ofisoshinsu da ke faɗin ƙasar har na tsawon kwana uku, tun daga ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, 2026, domin nuna alhini da girmamawa game da mutanen da suka sakamakon wannan lamari.

Bincike kan musabbabin mutuwar
Mutanen 37 sun mutu ne a ranar 17 ga Satumba, bayan da jami'an NSCDC suka kama su yayin wani samame kan haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto na Jihar Neja, a ranakun 15 da 16 ga Satumba.
Da farko, NSCDC ta ce ana zargin wata cuta ce ta ɓarke da ta haddasa mutuwar mutanen, tana mai cewa ana buƙatar gwaje-gwajen likitoci domin tabbatar da musabbabin mutuwar.
Sai dai an fara nuna damuwa kan yanayin da aka tsare mutanen, ciki har da zargin cunkoso da rashin isasshiyar iska a wurin da aka tsare su.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kwamandan NSCDC na Jihar Neja da wasu jami'an hukumar yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.
Hukumar ta ce jami'ai 24 suna hannunta domin gudanar da bincike kan rawar da suka taka wajen mutuwar mutanen.

Gwamnatin Tarayya ta kuma kafa kwamiti mai mambobi 10 domin gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin, ciki har da yadda aka kama mutanen, yanayin wurin da aka tsare su da kuma ainihin abin da ya haddasa mutuwarsu.
Lamarin ya haifar da zanga-zanga a Minna, babban birnin Jihar Neja, inda hukumomi suka sanya dokar hana fita bayan arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da wasu kungiyoyi sun bukaci gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen mutuwar mutanen.
NSCDC ta ce binciken da ake gudanarwa zai taimaka wajen gano abin da ya faru da matasan da aka tsare kana suka mutu, sannan ko akwai jami'an da ya kamata su fuskanci matakin ladabtarwa ko kuma shari'a.




















