| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Haka kuma, Hukumar Kula da Hana Shan Miyagun Kwayoyi ta Ghana ta kama mutane uku yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama


An kama mutum goma, ciki har da jami’an hukumar kwastam ta Ghana hudu, dangane da binciken da ake yi kan fasa-ƙwaurin kwayoyi ta hanyar tashoshin jiragen ruwa ta Ghana.

An bayyana wannan matakin ne yayin taron shugabannin tsaro wanda Shugaba John Dramani Mahama ya jagoranta a ranar Alhamis.

An yi wa Shugaba Mahama bayani game da binciken da ake gudanarwa a halin yanzu kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan da suka shafi zargin fasa-ƙwaurin ƙwayoyi zuwa wajen Ghana wadanda aka fita da su ta hanyar tashoshin jiragen ruwa na kasar.

Taron ya kuma duba tsare-tsaren tsaro da tsarin aiki da ake da su a halin yanzu a tashoshin jiragen ruwa tare da gano karin matakan karfafa iko da hana safarar kwayoyi.

A matsayin bangare na kokarin magance matsalar, Shugaba Mahama ya ba da umarnin kafa wata tawagar hadin gwiwa tsakanin hukumomi don bunkasa da mika cikakken tsarin a cikin makonni biyu, inda za a zayyana matakan hana fasa-kwaurin kwayoyi a kan iyakokin Ghana.

Wannan sabon tsarin ya biyo bayan kwace kusan tan 3.9 na hodar ibilis da jami’an kwastam na kasar Faransa suka yi a tashar jiragen ruwa ta birnin Dunkirk.

An ruwaito cewa an boye kwayoyin ne a cikin wata kwantena wadda aka ce tana dauke da sharar robobi da ta zo daga Ghana. Kwayoyin da aka kimanta kudinsu ya kai Yuro miliyan 225, an ce kwayoyin sun isa Faransa ne kan hanyarsu ne zuwa birnin Antwerp na kasar Belgium.

A kasar Ghana, Hukumar Kula da Hana Shan Miyagun Kwayoyi ta kama mutane uku yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.