Hukumomin tsaro sun kama wani mai PoS da ke sayar da kayayyakin babur a Ƙaramar Hukumar Matazu ta jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya, Isiyaku Nasiru, kan zargin taimaka wa wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Kachalla Muhammadu, wajen sarrafa miliyoyin nairori.
Dakarun tsarin jihar Katsina ne suka kama Nasiru tare da: Abubakar Sayaya da Nura Baka Sati da kuma Ubale Mai Cange, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jaridar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a wurare daban daban na jihar tsakanin ranar Alhamis da ranar Asabar.
Shugaban ƙaramar hukumar, Shamsuddeen Muhammad Sayaya, wanda ya tabbatar da kamen wa Daily Trust, ya ce waɗanda ake zargin an alaƙanta su ne da dabar ƙasurgumin ɓarawon dajin.
Ya ce ana bincike kan waɗanda ake zargin, yana mai jaddada cewa kamen zai iya bai wa jami’an tsaro bayanai da za su iya tona asirin tsarin da ke taimaka wajen ci-gaban aikata laifukan a yankin.
Ana zargin cewa an yi amfani da Nasiru a mastayin wani ɓangare na hanyar tura kuɗin da ke da alaƙa da Muhammadu ga masu sayo makamai da sauran kayayyakin buƙatu.
Matazu ta daɗe tana fama da kashe-kashe da garkuwa da mutane da raba mutane da gidajensu da lalacewar tattalin arziki da ya sa da ƙyar ake iya rayuwa a garin.
Kamar yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro a yankinm arewa maso yammacin Nijeriya, manoma da dama sun tsere daga gonakinsu domin tsoron garkuwada su.





















