| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Burkina Faso, Mali da Nijar sun shiga sahun neman karɓar baƙuncin Gasar AFCON ta 2032
Burkina Faso da Mali da Nijar, waɗanda suka kafa Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES), sun ce suna ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni kamar tsaro, ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.
Burkina Faso, Mali da Nijar sun shiga sahun neman karɓar baƙuncin Gasar AFCON ta 2032
Burkina Faso, Mali da Nijar sun shiga sahun neman karɓar baƙuncin Gasar AFCON ta 2032

Burkina Faso da Mali da Nijar sun ɗauki matakin farko na neman haɗin gwiwar karɓar bakuncin Gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2032, bayan da shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafarsu suka gudanar da wata ganawar farko da Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe, a birnin New York.

An gudanar da ganawar ne gabanin wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, bayan da CAF ta buɗe karɓar buƙatun ƙasashen da ke son karɓar bakuncin gasannin AFCON na shekarun 2028, 2032 da 2036.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Mali ta ce ƙasashen uku na shirin gabatar da ƙwararan takardun neman baƙuncin, waɗanda suka ginu kan haɗin kan yanki, haɗin kai tsakanin ƙasashe da kuma bunƙasa ƙwallon ƙafar Afirka.

Burkina Faso da Mali da Nijar, waɗanda suka kafa Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES), sun ce suna ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni kamar tsaro, ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.

Sai dai har yanzu ƙasashen uku na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro masu nasaba da ta'addanci.

Da yake magana bayan ganawar, Motsepe ya ce za a tantance ƙasashen uku bisa ƙa'idoji iri ɗaya da sauran masu neman baƙuncin.

Ya ce, "Za su samu dama irin ta kowace ƙasa." Ya ƙara da cewa CAF za ta yi la'akari da batutuwa kamar tsaro, ingancin ababen more rayuwa da kuma tabbatar da zirga-zirgar magoya baya cikin aminci kafin yanke hukuncin wace ƙasa za ta karɓi bakuncin gasar.

Burkina Faso ta taɓa karɓar bakuncin AFCON a 1998, yayin da Mali ta shirya gasar a 2002. Idan ƙasashen uku suka yi nasara, wannan ne karon farko da za su shirya gasar tare a matsayin masu haɗin gwiwar baƙunci.