Fiye da fasinjoji 3,000 da suka bi jiragen kamfanin Saudi Arabian Airlines daga Jeddah zuwa Kano da ke yankin arewancin Nijeriya na ci gaba da kokawa kan yadda kayayyakin suka maƙale a Saudiyya tsawon makkoni bayan dawowarsu gida.
Wasu daga cikin fasinjojin sun shaida wa manema labarai cewa daga cikin jakunkunan kayayyakinsu da aka bari har da tufafi da magunguna da takardun shaida da katunan ATM da makullan gidaje da na motoci a filin jiragen sama na Jeddah.
A cewar fasinjojin sun sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano kusan makonni biyu da suka wuce, amma suka tarar cewa ba a tawo musu da kayayyakinsu ba.
Kazalika wasu sun ce har da jakar hannu da ake ba da damar shiga da ita cikin jirgi ba a ba su ba.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta tabbatar da barin tulin kayan fasinjojin, inda ta ce kawo yanzu an shigo da kusan tan takwas na kayayyakin zuwa Nijeriya bayan shiga tsakani da ta yi.
Sai dai hukumar ta ce ana hasashen kusan tan 180 na kaya har yanzu suna Jeddah.
Fasinjoji sun koka kan rashin bayani daga Saudi Air
Ɗaya daga cikin fasinjojin, Injiniya Usman Ahmed Zun-Noorayne, ya shaida wa gidan rediyon Freedom cewa ya tafi Saudiyya domin aikin Umrah a ranar 1 ga Satumba, kuma ya dawo Nijeriya a ranar 15 ga Satumba.
Ya ce ba a yi wa fasinjojin bayani yadda ya kamata cewa ba za a tawo musu kayansu tare da su ba.
“Kafin mu shiga jirgi, aka gaya mana cewa mu karɓi jakarmu ta hannu idan muka sauka.”
Zun-Noorayne ya ce fasinjojin sun yi tsammanin za su karɓi kayansu bayan sauka a Kano, amma da suka je wajen karɓar kaya, sai suka tarar babu komai.
Ya ce wasu fasinjoji sun bar muhimman abubuwa kamar wayoyi, katunan ATM, takardun shaida da makullai a cikin jakunansu na hannu.
Kazalika wani fasinja maoi suna Babagana Muhammad, ya ce ya yi tafiya tare da matarsa daga filin jirgin Heathrow da ke London, inda kowannensu ya yi rajistar akwatuna biyu masu nauyin kilogram 23.
Ya ce sun isa Kano a ranar 17 ga Satumba, amma da suka isa wurin ɗaukar kaya a filin jirgin sai aka sanar da su cewa jirgin ya iso ba tare da kayan fasinjoji ba.
Kamfanin jirgi ya danganta lamarin da matsalolin gudanar da aiki
Fasinjojin da suka je ofishin Saudi Arabian Airlines a Kano sun ce an gaya musu cewa matsalolin gudanar da ayyukan jirage da suka shafi samar da man jirgin sun shafi zirga-zirgar jiragen daga Kano.
A cewar Zun-Noorayne, ba a ba fasinjojin takamaiman ranar da za a kawo musu kayansu ba.
Ya ce kamfanin jirgin ya bayyana cewa jirage suna da iyakar nauyin kayan da za su iya ɗauka, don haka aka fifita jigilar fasinjoji yayin da ake shirin kawo kayansu daga baya.
Kamfanin jirgin ya danganta matsalar da kalubalen ayyukan jirage da suka shafi samar da man jirgi daga Kano.
Sai dai hukumar filin jirgin saman Malam Aminu Kano ta ce ba a samu karancin man jirgi gaba ɗaya ba, amma tashar da kamfanin ke amfani da ita ce ba ta da mai.
NCAA ta ce Saudi Arabian Airlines ta amince da ware jirgi na musamman domin dawo da kayayyakin, tare da biyan diyya ga fasinjojin da suka shigar da ƙorafi ta tashar hukumar.






















