An samu Manchester City da laifin mummunar keta dokokin kuɗin Gasar Firimiya a cikin kaka tara, amma ƙungiyar ta ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Wata hukuma ta bincike mai zaman kanta ranar Talata ta samu City da laifin keta dokokin tsakanin kakar 2009-10 zuwa ta 2017-18, ciki har da shirya yarjejeniyoyi “na bogi” da abokan hulɗa na kasuwanci da rashin bayyana kuɗi yadda ya kamata da kuma ɓoye ainihin halin da asusunta yake daga masu bincike da kuma hukumomin ƙwallon ƙafa.
Kazalika hukumar ta gano cewa City ta kambama yawan kuɗaɗen shigarta tare da rage kuɗaɗen da take kashewa da fiye da dala biliyan 1.2, lamarin da ya bai wa ƙungiyar damar bayyana kanta a matsayin mai bin dokokin kuɗi.
Ta bayyana cewa City ta keta dokokin da suka taƙaita iya kuɗin da ya kamata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kashe a Gasar Firimiya da UEFA.
An kuma gano cewa City ta gaza sauke nauyin da ya rataya a kanta na ba da haɗin kai ga binciken Gasar Firimiya, inda aka tabbatar da zarge-zarge uku daga cikin huɗu.
Hukumar ta ce ƙungiyar ta yi yunƙurin hana binciken.
Shugaban Gasar Firimiya Richard Masters ya bayyana sharia’ar a matsayin shari’a’r ladabtarwar da ta fi muhimmanci a tarihin gasar, yana mai cewa abubuwan da aka gano sun tabbatar da cewa City ta ci gaba da keta dokoki a kusan shekara goma.
Kawo yanzu dai ba a tabbatar da hukuncin da za a yi wa ƙungiyar ba, kuma za a tabbatar da wannan ne a wani zama na daban.
Dokokin Gasar Firimiya sun ba da damar hukunci da suka haɗa da cin tara da rage maki da sauran hukunce-hukunce na wasanni.
Manchester City ta ce ta “ji takaici da kuma mamakin” hukuncin kuma ta bayyana cewa ba ta aikata wani laifi ba, tana mai cewa hukuncin na da “kurakurai a bayyane ” na doka da ƙ’aida da gaskiya.
Ƙungiyar ta tabbatar da cewa za ta bi dukkan hanyoyin ɗaukaka ƙara.
Tana iya ɗaukaka ƙara daga yanzu zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.




















