| Hausa
NIJERIYA
4 minti karatu
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar ga al’ummar Nijeriya a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
"Sauye-sauyen ba su ne suka haifar da rugujewar tattalin arzikinmu ba,'' in Shugaba Tinubu a jawabinsa na ranar tuni da 'yancin kan Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa jerin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi tabbas za su haifar da sakamako mai kyau nan gaba.

Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a jawabin da ya gabatar wa al’ummar ƙasar a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kai.

Shugaban ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi ba su ne suka durƙusar da tattalin arzikin ƙasar kamar yadda ake zargi ba. Ya tabbatar da cewa alƙawuran da ya yi wa 'yan Nijeriya sun soma cika.

“Lokacin da wannan gwamnatin ta hau mulki, mun ƙuduri aniyar gyara abubuwa da dama.

Mun zaɓi mu cire kitse daga wuta. Tabbas an sha wahala a sauye-sauyen da suka biyo baya. Illolin sun bayyana. Amma duk da haka, ba za mu taɓa haɗa maganin da cuta ba.

"Sauye-sauyen ba su ne suka haifar da rugujewar tattalin arzikinmu ba.

Masu AlakaTRT Afrika - ‘Yan Nijeriya fiye da 67,000 sun amfana da shirin ba da lamuni ga ƙananan masana'antu – Tinubu

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya magance irin matsalolin da suka taru tsawon shekaru masu yawa a cikin shekaru huɗu ba.

Ya ce ya san cewa iyali da dama har yanzu suna fuskantar ƙalubale wajen neman abinci, kuɗin makaranta, kuɗin magani, da na sufuri amma dole a ɗauki tsauraran matakai yanzu domin gaba ta yi kyau.

Ya ƙara da cewa waɗannan ƙalubale ba su faro daga tsare-tsaren gyara na shekaru uku da suka wuce ba, a’a, sun samo asali ne daga shekaru da dama na rashin ci gaba da rashin ababen more rayuwa da manyan cibiyoyi da rashin damarmaki ga jama’a marasa karfi.

“Za mu iya gina tattalin arziƙin da ke tsamo mutane daga cikin talauci a hankali a hankali, tare da tabbatar da cewa ba a manta ko watsar da waɗanda ke tsakiyar waɗannan matsaloli ba a kan tafiyar.”

“Yanzu, yayin da wasu masu tasiri ke kira da a koma ga tallafin mai da ke da tsada kuma ke haifar da matsaloli, dole ne mu yi tsayin daka. Ya kamata mu tuna dalilin da ya sa muka fara waɗannan sauye-sauye da kuma irin ci gaban da muka samu zuwa yanzu.

“Bayan shekaru uku da rabi, babu shakka cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya inganta. Tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru da kashi fiye da 4 cikin 100 a bana. Ɓangaren man fetur da sauran ɓangarorin da ba na man fetur ba, duk sun taimaka wajen dawo da ci gaba mai ɗorewa.”

Shugaban ya ce satar man fetur a ƙasar ta ragu, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ita ma ta “ragu sosai”.

“An samu raguwar satar man fetur. Hauhawar farashin kayyayyaki ta ragu sosai. An kuma sake gina asusun ajiyar ƙudaden waje na Nijeriya.

“Kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta samu daidaito. A shekarar 2025, Nijeriya ta samu kuɗaɗen shiga mafi yawa a tarihinta daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba, inda kuɗaɗen suka haura dala biliyan 6. Waɗannan kuɗaɗe ne da kamfanonin Nijeriya suka samu ta hanyar kasuwancinsu.”

“Waɗannan ba maganganun da ba su da hujja ba ne. Masu sa ido na ƙasa da ƙasa da ’yan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin ƙasa da ƙasa suna ganin sauyin da aka samu.

Kowannensu ya fahimci cewa sauye-sauyenmu sun ƙarfafa daidaito da juriyar tattalin arzikin Nijeriya. Kamfanoni masu zaman kansu ma sun daɗe da tabbatar da hakan, yayin da hannayen-jarin ƙasashen waje ke ci gaba da ƙaruwa a kowace shekara.”

Ya jaddada cewa ƙasar ta kai wani muhimmin mataki na samun wadata.

“Lokacin matakan gaggawa ya wuce. Mun gyara tubalin tattalin arzikinmu. Mun samu sauyi a babban aikin da ke gabanmu a yanzu. Tsawon shekaru uku, babban burinmu shi ne gyara tafarkin ƙasar nan.

“Yanzu kuma burinmu a bayyane yake, samar da wadata ga kowa, wadda za ta yaɗu zuwa ga al’umma baki ɗaya.”