| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Jikana bai shirya yin aiki a kamfaninmu ba a yanzu, in ji Dangote
Dangote ya ce matashin jikansa na farko, wanda injiniyan lantarki ne, yana son fara samun kwarewar aiki a wajen rukunin kamfanonin Dangote kafin daga bisani ya shigo a dama da shi a kamfanin iyalin Dangote.
Jikana bai shirya yin aiki a kamfaninmu ba a yanzu, in ji Dangote
Jikana bai na son samun kwarewa a wajen kamfanin iyalinmu, in ji Dangote

Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce jikansa na fari ya ce a halin yanzu bai shirya shiga harkokin kasuwancin iyalinsu ba.

Dangote ya ce matashin, wanda injiniyan lantarki ne, yana son fara samun ƙwarewar aiki a wani wuri na daban sannan daga bisani ya shiga a dama da shi a kamfanonin iyalin Dangote.

Babban ɗan kasuwar ya bayyana hakan ne a wani taron ganawa da masu zuba jari da aka gudanar a Nairobi, Kenya, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen fara sayar da hannayen-jarin matatar man Dangote ga jama'a.

Dangote ya ce jikansa na duba yiwuwar yin aiki da kamfanonin hada-hadar kuɗi da tantance asussan kamfanoni na duniya irin su KPMG ko PwC, domin samun ƙwarewa.

Masu AlakaTRT Afrika - Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16

“Yana son ya je ya samu ƙwarewa a KPMG ko PwC. Daga nan sai ya dawo a dama da shi a kamfaninmu,” in ji Dangote.

Kazalika ɗan kasuwar ya gabatar da ‘yarsa ta fari, Mariya Dangote, da mijinta Alassane, waɗanda suka halarci taron, yana mai kwatanta Mariya da mace mai kunya.

Dangote ya ce tuni ‘ya’yansa mata uku Mariya da Halima da kuma Fatima suka soma taka rawa wajen gudanar da harkokin kamfanoninsa, inda suke riƙe da muƙamai na zartarwa a sassa daban-daban na rukunin kamfanonin.

Rukunin kamfanonin Dangote na da harkoki a ɓangarorin siminti da sukari da tace man fetur da takin zamani da masana'antu.

Dangane da shirin tsare-tsaren mika ragamar shugabancin kamfanin, Dangote ya ce kamfanin ya fi mayar da hankali kan tsari na shekaru biyar, maimakon shekaru 10.

Ya bayyana cewa tsawaita wa’adin na iya sa ma’aikata da shugabannin kamfanin su yi sakaci wajen cim ma ayyukan da ake buƙata, saboda la’akari da nisan loakcin da aka sanya.

A baya, Dangote ya taɓa bayyana cewa samun magaji namiji ba shi ne babban abin da ya fi ba shi muhimmanci ba, inda ya ce kamata ya yi a mayar da hankali kan ƙwarewa da kuma makoma gaba wajen jagorancin kamfanin, ba wai kan jinsi ba.