Azzedine Ounahi ya zura ƙwallo a raga sau biyu inda ya jagoranci Maroko a nasararta ta ci uku da nema a kan Kanada a zagaye na ƙasashe 16 na gasar cin kofin duniya, lamarin da ya mayar da ƙasar ƙasa ta farko a Afirka da ta fara kaiwa matakin kusa da daf da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya sau fiye da ɗaya .
Wannan shi ne lokaci na biyu a jere da ƙasar ta kai wannan matakin bayan ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta fara kaiwa matakin daf da na ƙarshe a gasar a shekarar 2022.
Tun da aka fara wasan dai babu wata tawaga da ta samu ta zura ƙwallo a raga har sai da Ounahi ya zura ƙwallon da Achraf Hakimi ya bugo daga bugun tazara daga wajen murabba’in fenareti, lamarin da ya saka Maroko a gaba da ƙwallo a ɗaya minti 50 da fara wasa.
Ounahi ya zura ƙwallo na biyu a raga daga tsakiyar murabba’in daga wani fasin da Brahim Díaz ya masa minti 82 da fara wasa .
Soufiane Rahimi ya ƙara ƙwallo na uku a mintin ƙarshe na wasa.
Yanzu Maroko ta tafi matakin daf da na ƙarshe inda za ta haɗu da Faransa ranar Alahamis a filin wasa na Boston.
Kayen da Kanada ta sha ya kawo ƙarshen tafiyar bajintan ɗaya daga cikin ƙasashe masu masauƙin baƙi a gasar cin kofin duniyar, inda ƙasar ta samu ta yi nasararta ta farko a matakin sili ɗaya ƙwale a tarihinta na gasar a nasarar ci ɗaya da nema da ta yi kan Afirka Ta Kudu kafin ta kai ga wasan da aka yi ranar Asabar.








