| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Masar ta zargi Habasha da siyasantar da aikin Madatsar Ruwan GERD
Masar ta zargi Habasha da gudanar da aikin madatsar cikin “salon siyasa” ba tare da tuntubar ƙasashen da ruwa ke gangarawa zuwa gare su ba, wato Masar da Sudan, yana mai gargadin cewa irin waɗannan matakai sun haifar da “mummunan tasiri sosai.”
Masar ta zargi Habasha da siyasantar da aikin Madatsar Ruwan GERD
Masar da Sudan sun daɗe suna takaddama da Habasha kan yadda ake gudanar da aikin GERD

Masar ta zargi Habasha da “siyasantar” da gudanar da aikin Babbar Madatsar Ruwan Renaissance ta Habasha (GERD) da ke kan Kogin Nilu ta hanyar ɗaukar matakai ita kaɗai da suka shafi Masar da Sudan.

Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya yi tare da Ministan Harkokin Wajen Mozambique, Manuela Lucas, a birnin Alkahira ranar Litinin.

Abdelatty ya bayyana tsaron ruwa a matsayin batu na rayuwa ko mutuwa ga Masar kuma babban fifiko na ƙasa, yana mai cewa “ba za a iya yin sassauci a kansa ba.”

Ya ce Masar ta sha yin gargadin cewa Habasha ta gina madatsar ruwan ne ta hanyar ɗaukar matakai ita kaɗai ba tare da la’akari da dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ƙa’idar tuntubar sauran ƙasashe kafin ɗaukar mataki ba.

Ya ƙara da cewa “Habasha, a matsayin ƙasar da ruwa ke gangarowa daga gare ta, ba za ta iya yin aiki ita kaɗai ba.”

Ya zargi Habasha da gudanar da aikin madatsar ruwan cikin “salon siyasa” ba tare da tuntubar ƙasashen da ruwa ke gangarawa zuwa gare su ba, wato Masar da Sudan, yana mai gargadin cewa irin waɗannan matakai sun haifar da “mummunan tasiri sosai.”

Raguwar adadin ruwa

A cewar Abdelatty, matakin da Habasha ta ɗauka na riƙe ruwa ba tare da tuntubar sauran ƙasashen ba ya janyo raguwar matakin ruwa a Sudan a cikin kwanakin baya-bayan nan, lamarin da ya shafi samun ruwa ga al’ummomin Sudan.

Ya jaddada cewa Masar “ba ta adawa da haƙƙin Habasha na ci gaba da bunƙasa ƙasa, muddin hakan ba zai cutar da Sudan ko Masar ba,” yana mai cewa: “Suna da haƙƙin ci gaba, mu kuma muna da haƙƙin rayuwa.”

Masar da Sudan sun daɗe suna takaddama da Habasha kan yadda ake cika da gudanar da aikin GERD, wanda Habasha ta fara ginawa a shekarar 2011 kuma ta ƙaddamar da shi a hukumance a watan Satumban 2025.

Alkahira da Khartoum sun yi kira da a cimma wata yarjejeniya mai ɗorewa ta ƙasashe uku da za ta tsara yadda za a cika da gudanar da madatsar ruwan kafin a kammala aikin.

Sai dai Habasha ta dage cewa aikin ba ya buƙatar wata yarjejeniya mai ɗorewa, kuma ta nace cewa ba ta da niyyar cutar da muradun kowace ƙasa.

Takaddamar ta sa an dakatar da tattaunawar ta tsawon shekaru uku kafin a sake komawa teburin sulhu a shekarar 2023, amma tattaunawar ta sake tsayawa a shekarar 2024.