Ministocin harkokin waje na Saudiyya da Pakistan da kuma Turkiyya sun tattauna kan shirye-shiryen taron gaggawa na manyan hafsoshin sojin ƙasashen uku don duba hanyoyin tallafa wa Saudiyya a ƙarƙashin shirin yarjejeniyar tsaro ta Makka, a cewar rahoton da kafar watsa labarai ta Saudi Gazette ta fitar.
Yarima Faisal bin Farhan, da Ishaq Dar da kuma Hakan Fidan sun yi zaman shawarwari a hedkwatar ofishin jakadancin Saudiyya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke New York.
Ministocin sun yi bita kan shirye-shiryen da ake ci gaba da yi na taron shugabannin jami’an tsaron, wanda zai binciki hanyoyin tallafawa Saudiyya bisa ga alƙawarin da aka ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar tsaro.
Yarjejeniyar Makka ta tanadi cewa hari kan kowace ƙasa ɗaya daga cikin ƙungiyarta ya zama tamkar hari ne ga dukkan ɓangarorin.

A yayin zaman bitar, ministocin sun "yi Allah wadai da" hare-haren da aka kaiwa Makka da kuma cibiyoyin farar hula da tattalin arziki a Saudiyya.
Sun tattauna sabbin abubuwan da suka faru a yankin kana sun jaddada muhimmancin kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa, da kyakkyawar alaƙa ta maƙwabta, da girmama ikon mallakar ƙasa da kuma rashin tsoma baki a harkokin cikin gida.
Kazalika sun kuma jaddada muhimmancin tabbatar da tsaro da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa.
Ministocin sun sake jaddada alƙawarinsu na yin aiki don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin, tare da tallafa wa ƙoƙarin hanyoyin rage tashin hankali da kuma haɓaka hanyoyin magance rikice-rikicen da ke ci gaba da faruwa.


















