Ghana, wadda ta jagoranci wani yaƙin neman biyan diyya kan cinikin bayi na ƙetare Tekun Atlantika da ya ɗauki kusan ƙarni huɗu ana yi, ta ce ƙasashen Yammacin duniya na ƙara nuna goyon baya ga wannan yunƙuri.
Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar kan adalcin biyan diyya, wanda Ghana, Jamus da Faransa suka shirya tare a gefen taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Laraba.
Ya ce matakin farko na wannan yaƙin neman biyan diyya shi ne mayar da kayayyakin tarihi da aka wawashe.
Ya ƙara da cewa matakai na gaba na iya haɗawa da neman afuwa a hukumance, sassauta ko rage basussuka da kuma biyan diyya ta kuɗi, ƙarƙashin wani shiri mai ɗauke da matakai 19 da Tarayyar Afirka da Kwamitin Ƙasashen Caribbean kan Adalcin Biyan Diyya suka amince da shi a wani taro da aka gudanar a Ghana a watan Yuni.
A watan Maris, Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da wani ƙuduri da ya ayyana bautar da aka yi ta hanyar safarar bayi waɗanda aka ƙetare Tekun Atlantika da su a matsayin “babban laifin da aka taɓa aikatawa kan bil’adama”, inda ƙasashe 123 suka kada ƙuri’ar amincewa, yayin da uku — Amurka, Isra’ila da Argentina — suka ƙi amincewa. Wasu ƙasashe 52, ciki har da ƙasashen Tarayyar Turai da Birtaniya, sun kaurace wa ƙuri’ar.
Ƙasashen da ke tuntuɓar Ghana
Ablakwa ya ce tun daga lokacin, ƙasashen Turai da dama sun bayyana goyon bayansu ga wannan yunƙuri.
“Cikin kusan dukkan ƙasashen Turai da suka kaurace wa ƙuri’ar a lokacin, sun tuntube mu kuma sun ce za su yi aiki tare da mu a wannan tafiya,” in ji Ablakwa.
Ya ce Birtaniya da Portugal sun yi tayin bayar da goyon baya, yayin da Amurka ita ma ta ce a shirye take ta yi aiki tare da yunƙurin da Ghana ke jagoranta.
Ablakwa ya ƙara da cewa Faransa, Jamus da Netherlands sun yi alkawarin shirye-shiryensu na mayar da kayayyakin tarihi da aka kwashe.
“Mayar da waɗannan kayayyaki na da matuƙar muhimmanci a wannan tafiya... Ya kamata a mayar da waɗannan kayayyakin tarihi zuwa ƙasarsu ta asali,” in ji ministan.
A cewar bayanan da ke cikin Rumbun Bayanai na Cinikin Bayi na Ƙetare Tekun Atlantika, an bautar da kusan ’yan Afirka miliyan 12.5 tare da jigilar su ta ƙetare Tekun Atlantika tsakanin ƙarni na 16 da na 19.
An kai waɗannan mutanen zuwa Kudancin Amurka, yankin Caribbean da Arewacin Amurka, inda aka tilasta musu yin aiki a gonaki da ma’adinai. Wannan cinikin bayi ya samar da ɗumbin arziƙi da ya taimaka wajen bunƙasar ƙasashen Yammacin duniya.
A cewar wannan rumbun bayanai, Portugal da Birtaniya ne ke da alhakin jigilar fiye da kashi 70 cikin 100 na dukkan ’yan Afirka da aka bautar waɗanda aka ƙetara tekun Atlantika da su.




















