Shugaban gwamnatin riƙo na Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya yi rangadi game da shirin sojin ranar Laraba a jihar Blue Nile da ke kudu maso gabashin Sudan.
Ziyarar na zuwa ne a cikin yanayi na ƙarin arangama tsakanin sojin ƙasar da dakarun RSF da ƙawarta, SPLM-N.
A wata sanarwa, rukunin sojin ƙasa na huɗu na ƙasar ta ce Burhan, wanda ke jagorantar sojin Sudan, ya ziyarci birnin Damazin, babban birnin jihar da kuma hedikwatar ɓangaren sojin.
Ta ƙara da cewa Burhan ya yi rangadin dakarun rukunin sojin ne kuma ya yi nazari kan shirinsu kuma ya yi nazari kan shirin yaƙinsu na iya aiwatar da ayyukan da aka ba su.
‘Mayar da hankali da horo ’
Ya kuma yi bayani a kan yanayin tsaro da na aiki yankin, in ji sanarwar.
Burhan ya jaddada “buƙatar ɗaga matakin shiri da mayar da hankali da kuma ƙarfafa horo da shirin yaƙi ," in ji sanarwar.
Ya kuma yi kira da “ci-gaba da ayyukan bisa shiri da umarnin soji."
Burhan ya kuma yi rangdin asibitin soji na Damazin, inda aka masa bayani game da yanayin sojojin da suka ji rauni da mara lafiya, da kuma ayyukan asibitin.
‘Cikin cikakken shiri’
Ya tabbatar da jajircewar shugabancin rundunar sojin kan jami’anta da kuma ba su kulawa da ya dace.
Sanarwar ta ambato kwamandan rukunin sojin ƙasa na huɗu, Manjo Janar Ismail al-Tayeb, wanda ya ce ziyarar Burhan “ ta ƙarfafa shirinsu na aiwatar da ayyukansu.”
“Dakarun rukunin suna cikin cikakken shiri domin aiwatar da ayyukansu na soji da tsare yankin da kuma kare fararen hula,” in ji shi .
Ya ƙara da cewa rukunin ya shirya domin “ci-gaba da aiwatar da shirye-shirye da umarnin da rukunin ya bayar.”
Ziyarar Burhan na zuwa ne cikin wani yanayi da lammura na soji ke faruwa cikin sauri a jihar Blue Nile.
Ranar Talata, kashi na farko na dakarun haɗin gwiwa daga ƙungiyoyin da ke da alaƙa da sojin ya isa jihar Blue Nile.
Kakkaɓo jirage mara matuƙa
A ranar Asabar, rundunar sojin ta bayyana cewa ta tura wani birgedi na manyan sojoji da ke da alaƙa da Hukumar Tattara Bayanan sirri a fagen yaƙi a yankin Bakori na jihar.
Rundunar sojin ta kuma bayyayan aranar Alhamis da ta gbata cewa ta kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi na “hamayya” a jihar Blue Nile bayan ya ƙetare kan iyaka daga ƙasar Ethiopia.
Ta ƙara da cewa shi ne jirgi mara matuƙi na uku da ta yi shelar kakkaɓowa a cikin mako ɗaya.
Baya ga Blue Nile da yankin Darfur a yammacin Sudan, ana ci gaba da yaƙi a jihohi uku na Kordofan - jihohin North da West da kuma South na Kordofan - tsakanin soji da dakarun RSF tun watan Oktoban shekarar 2025.
Sudan tana fuskantar waƙi tsakanin soji da rundunar RSF tun watan Afrilun shekarar 2023, wanda ya kashe gomman dubban mutane tare da raba kimanin mutum miliyan 13 da gidajensu, in ji kiyasi na Majalisar Ɗinkin Duniya da na ƙasa da ƙasa.























