| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin wani taro da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yanjarida.
EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya
EFCC

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Masu Laifin Tattalin Arziki ta Nijeriya, EFCC ta ce ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa da kuma almundahana cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin wani taro da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yanjarida.

Ya ce fiye da biyar daga cikin ma’aikatan da aka kora a halin yanzu suna fuskantar shari’a, yayin da ake shirya takardun shari’ar wasu da ake zargi da aikata laifuka.

Olukoyede ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa ma’aikatan hukumar suna bin ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana.

Hukumar ta kuma ƙaddamar da dokar karɓar kyaututtuka, wadda ke buƙatar ma’aikata su bayyana kadarori da kyaututtukan da suka wuce wani ƙayyadadden ƙima, ciki har da kyaututtukan da suka samu daga ’yan’uwa da ke ƙasashen waje.

Haka kuma, EFCC ta sauya sunan tsohon Sashen Harkokin Cikin Gida zuwa Sashen Da’a da Riƙon Amana, domin ƙarfafa sa ido da ɗa’a a cikin hukumar.

Olukoyede ya kuma bayyana cewa EFCC ta ƙwato kusan naira tiriliyan 1.23 da dala miliyan 684.48 da fam 373,905 da kuma euro miliyan 9.34 tsakanin 1 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yuni 2026.

Daga cikin kuɗin naira da aka ƙwato, kusan N397.26 biliyan an kwato su kai tsaye ga gwamnatin tarayya, yayin da N836.34 biliyan aka kwato a madadin ma’aikatun gwamnati, hukumomi, jihohi, kamfanoni, da wasu mutane da waɗanda laifukan suka shafa a ƙasashen waje.

Ya ce fiye da N661 biliyan da dala miliyan 492 daga cikin kuɗin da aka ƙwato an riga an miƙa su ga waɗanda suka cancanci karɓa.

Shugaban EFCC ya jaddada cewa ma’aikatan hukumar ba za su iya yaƙar cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba, alhali su kansu suna aikata irin wannan laifi.

Rumbun Labarai
Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya ya matsa ƙaimi don ceto waɗanda aka sace a masallacin Jihar Neja
'Yansandan Nijeriya sun kama likitoci kan zargin safarar mutane da cire musu ƙoda
Amurka na shirin janye sojojinta 200 da ta tura Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta gargaɗi al’ummomi 915 a jihohi 19 kan barazanar ambaliyar ruwa
Sufeta Janar na ’Yansandan Nijeriya ya tura AIG zuwa jihar Neja don ceto masallatan da aka sace
EFCC za ta ba da ladan kashi 5 cikin 100 ga wanda ya ba da bayanai kan kadarorin sata da ke ƙetare
Hedikwatar tsaron Nijeriya ta tattauna da jakadan Saudiyya kan ƙarfafa alaƙar tsaro
Masu garkuwa da mutane a Nijeriya sun tara naira biliyan 7 na kuɗin fansa: Bincike
Ranar Hausa ta Duniya: Harshen Hausa ya gawurta, in ji Shugaba Tinubu
Shaguna aƙalla 300 sun ƙone a gobarar da ta tashi a  kasuwar Oranyan da ke Ibadan a Nijeriya
Dawo da tallafin fetur zai mayar da Nijeriya baya a cigaban tattalin arzikinta — Minista
Wani bidiyo ya nuna mutum 600 da aka yi garkuwa da su a wani harin masallaci a jihar Neja a Nijeriya
NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekara 101 da tabar wiwi a cikin garin alabo
Dakarun Nijeriya sun kashe fiye da 'yanta'adda 20 a samamen da suka kai Borno
Za mu tabbatar Tinubu ya lashe zaɓen Nijeriya na 2027— Abdulaziz Yari
Tinubu ya buƙaci jami'an yaƙin neman zaɓensa su bayyana wa ‘yan Nijeriya nasarorin gwamnatinsa
Tinubu ya yi umarnin kama wani mutum, ya dakatar da manyan sakatarori bayan gano wata hukuma ta bogi
EFCC ta janye ƙarar da ta shigar da Maryam Shehu da Abubakar Shuraim kan zargin ɓata suna
Iyalai sun yi zanga-zanga a Nijeriya kan yaran da aka sace kusan kwanaki 100 da suka gabata
Kira a mayar da tallafin fetur jahilci ne kan yadda ake tafiyar da tattalin arziki - Tinubu