Wani hari da Amurka ta kai a Tsibirin Larak da ke kudancin Iran ya kashe mutane da dama tare da jikkata wasu dakarun Rundunar Kare Juyin-Juya-Halin (IRGC) da fararen hula da dama, a cewar dakarun, wadanda suka yi alƙawarin mayar da martani da "hukuncin mai tsauri".
A cikin wata sanarwa da aka fitar, sashen hulda da jama'a na IRGC ya zargi Amurka da kai hari "mai muni" a tsibirin da ke lardin Hormozgan a kudancin ƙasar a ranar Lahadi.
‘‘Abokan gaba na Amurka da Isra’ila wadanɗa suka gagara warware matsalolinsu na cikin gida da kuma raguwar aminci da suke da shi a tsakanin ƙasashe a yankin, a wani mataki na ƙoƙarin nuna rawar da suke takawa, sun kai wani mummunar hari Tsibirin Larak, inda suka kashe tare da jikkata mayakanmu da 'yan ƙasarmu da dama," in ji sanarwar.
A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Fars na Iran ya fitar, mai magana da yawun IRGC, Sardar Mohebi, ya zargi Amurka da aikata "mummunan kuskure kuma mai hatsari", wanda zai haifar da sakamako "a fannin tattalin arziki da na soja".
Da farko dai, Fars ya ba da rahoton cewa mazauna yankin sun ji fashewar wani abu kusa da Tsibirin Larak, yayin da ba a tabbatar da ainihin wurin da abin ya faru ba.
Rahotanni daga Iran sun zo ne bayan da kafofin watsa labarai na Amurka suka ce sojojin Amurka sun kai hari kan tsibirin, inda aka bayyana yanda sojoji suke shirin harba rokoki da bama-bamai zuwa cikin Mashigar Hormuz.
Rundunar Sojin Amurka ta kammala wani aiki na kawar da nakiyoyin ruwa daga hanyoyin jigilar kaya na kasa da kasa ta hanyar mashigar ruwan a makon da ya gabata, a cewar gwamnatin Trump.
A ranar Talata shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa "An sanar da Iran cewa duk wani jirgi ko kwale-kwale da ke dauke da nakiya za a lalata shi nan take kuma cikin tsari."
"Sojojin Amurka suna sa ido sosai kan yankin kuma a shirye suke don kare 'yancin zirga-zirgar jiragen kasuwanci ta wannan muhimmin hanyar ruwa," a cewar wani jami'in Amurka.
Tun da farko, Kakakin Majalisar Dokokin Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya yi watsi da ikirarin Sakataren Baitulmalin Amurka Scott Bessent kan cewa, matakan Washington na tattalin arziki da kuma rufe mashigar Hormuz za su murƙushe tattalin arzikin Iran.
"Maƙaryaci, maƙaryaci, wando na ci da wuta," in ji Ghalibaf a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai mayar da martani ga ikirarin Bessent cewa Washington ta kawo ganga miliyan 130 na mai zuwa kasuwa a cikin kwanaki 14 da suka wuce.























