Gwamnatin Nijeriya ta bayyana matuƙar damuwa kan halin siyasa da tsaro da ake ciki a maƙabciyarta Jamhuriyar Nijar, bayan wani yunƙurin juyin mulki da aka ruwaito a babban birnin ƙasar, Niamey a ƙarshen makon da ya gabata.
Gwamnatin ta ce lamarin ya matuƙar tayar da hankali musamman ganin irin kyakkyawar alakar tarihi da zumunci da kuma al'adu da ke tsakanin Nijeriya da Nijar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar ta Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya da aka fitar ranar Lahadi a Abuja da ke ɗauke sa sannun mai magana da yawun ma’aikatar, Oluwafemi Adeniyi.
“Gwamnatin Nijeriya na nuna matukar damuwarta game da yanayin siyasa da tsaro da ake ciki yanzu a Jamhuriyar Nijar,” in ji sanarwar.
Gwamnatin mulkin Soji ta Nijar ta ce, ta sake ƙwace iko da muhimman wurare da aka kai hare-hare bayan yunƙurin wargaza ƙasar da wasu sojoji masu tayar da ƙayar baya suka yi a wata arangama da jami'an tsaro a Niamey a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce arangamar ta faru a wasu muhimman wurare, ciki har da fadar shugaban ƙasa da Filin Jirgin Sama na Diori Hamani da kuma sansanin sojojin sama na 101, wani sansanin sojoji mai mahimmanci a Yamai, da kuma wasu wurare a babban birnin.
Gwamnatin sojin Nijar ta bayyana lamarin a matsayin wani “yunkurin kawo ruɗani da tayar da zaune tsaye”, tana mai cewa an shawo kansa.
A ɓangare guda kuma, Gwamnatin Nijeriya ta ce tana fatan ganin an samu zaman lafiya da tsaro da dimokuraɗiyya da kuma ci-gaba a Nijar.
Ta kuma jaddada cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar zai yi tasiri kai-tsaye ga Nijeriya da ke zama makwabciyarta da yankin Afirka ta Yamma da kuma yankin Sahel.
Kazalika sanarwar ta ce, “Amfani da duk wani nau’i na ƙarfi wajen warware saɓanin siyasa zai kawo cikas ga cim ma wannan ƙuduri.”
Saboda haka, ‘‘Nijeriya na kira ga gwamnati da al'ummar Nijar da su haɗa kai domin samar da tsarin da za a dama da kowa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tsarin doka na ƙasa.’’
Nijeriya ta ce hakan yana da matuƙar muhimmanci ga makomar Nijar da zaman lafiyarta a yankin da kuma yankin Sahel baki ɗaya.





















