Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya bayyana ranar Alhamis cewa gwamnonin jihohin ƙasar sun sha alwashin rage tsadar ababen hawa a faɗin ƙasar bisa radin kansu.
Ya bayyana cewa za a kafa kwamitin haɗin gwiwa na gwamnatin tarayya da na jihohi nan take domin tabbatar da cewa iskar gas ta CNG mai araha ta samar da arahan ababen hawa daga ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2026.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Alhamis da taken ‘Dole Ƙarin Arahar Mai Ta Samar Da Arahar Ababen Hawa Shugaban Tinubu da Gwamnoni Na Ƙoƙarin Rage Tsadar Ababen Hawa a Faɗin Ƙasa,’ Shugaban ya ce tattaunawarsa da ƙungiyar gwamnonin Nijeriya da ranar Alhamis ta samar da jajircewa mai ƙarfi daga gwamnonin cewa za su yi amfani da fa’idar arahar CNG da motoci masu amfani da lantarki wajen rage tsadar ababen hawa a cikin jihohinsu.
“Na yi farin ciki da tattaunawa da Ƙungiyar Gwamnoni a wannan rana. Gwamnonin sun, bisa raɗin kansu, sha alwashin ɗaukar matakai nan take domin rage tsadar ababen hawa a jihohinsu, inda za su mayar da hankali kan amfani da fa’idojin CNG da motoci masu amfani da lantarki.”
Ya bayyana matakin zuba jarin da Gwamnatin Tarayyar ke yi a harkar sauya salon amfani da makamashi ta tsarin Shugaban ƙasa na amfani da iskar gas ta CNG.
“Gwamnatin Tarayyar ta riga ta fara zuba jari da yawa a wannan tsarin sauya salon amfani da makamashi.
“Ta hanyar Tsarin Shugaban ƙasa ta Iskar gas ta CNG, an sauya fiye da motocin bas 120,000 a fadin ƙasar [zuwa masu amfani da CNG], yayin da ƙarin fiye da kayayyakin sauyi 100,000 ke kan hanya.
“A lokaci guda, muna ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin sauya motocin da kuma shan man a faɗin ƙasar,” in ji shi.
Tinubu ya ce a halin yanzu fiye da ayyukan iskar gas 100 ake yi a fadin ƙasar ciki har da manyan tashoshin CNG 15 da ƙananan tashoshin CNG 86, yana mai tunawa cewa shi ya ƙaddamar da huɗu daga cikin ayyukan a Legas da Abuja da Owerri a watan Mayu.
“Wannan ya haɗa da tashoshi 15 na ƙara cika tukunyar CNG a Legas da kuma wani wuri a Abuja da zai iya hidima wa motoci da adaidaita sahu 1,000 da manyan motoci da bas 50 a yini,” a cewar Tinubu.
Shugaban ya yi shelar ƙara faɗaɗa shirin, yana mai cewa, “Na kuma ba da umarnin ƙarin tashoshin sake cika tukunyar CNG 500 a faɗin ƙasar, bayan tashoshi 500 da na ba da umarnin yi daga farkon shekarar,” yana mai cewa wannan zai mayar da tashoshin 1000 fadin ƙasar.
Shugaban ya bayyana cewa ya ɗaura wani ɓangare na alhaƙin aikin kan jihohi ne saboda a ababen hawa na cikin jihohi ne tsadar mai ya fi tasiri kan ‘yan Nijeriya, inda jihohi suka fi ƙarfin sa ido.
Shugaban ya ce, “Sufuri a cikin jiha shi ne inda ‘yan Nijeriya suka fi jin tsadar kuma nan ne jihohi suka fi ƙarfi. Na ji ƙwarin gwiwar cewa gwamnoninmu suna ƙoƙarin kawo waɗannan fa’idojin kusa da mutane da suke yi wa hidima.”
Ya bayyana cewa za a kafa wani kwamitin Gwamnatin Tarayyar da na Jihohi domin fara ƙaddamar da matakan.
Ya kuma nuna matakin rarar da za a iya samu, yana mai cewa tsarin tattalin arziki na amfani da iskar gas na CNG bai bar wata hujja ta ci gaba da kasancewar kuɗin mota ya tsaya yadda yaka a da ba.
Fetur ya fi CNG tsada da kashi 60 zuwa 80 cikin 100
“Mun yarda mu kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatotin jihohi domin fara ƙaddamar da waɗannan matakan nan take. Motar da ke amfani da CNG na kashe abin da ya gaza kashi 60 zuwa 80 cikin 100 na wanda ke amfani da fetur da kashewa.
“Daga ranar 1 ga watan Oktoba, burin mu shi ne ‘ya Nijeriya su fara cin moriyar wannan rarar ta hanyar raguwar kuɗin ababen hawa. Mun yarda cewa ya kamata arahar mai ta samar da arahar ababen hawa,” in ji shi.
Shugaban ya yi kira da a ɗauki matakai na bai ɗaya a duk matakan gwamnati domin cika alƙawarin, yana mai cewa “Dole duk wani matakin gwamnatin ya ci gaba da yin nashi ɓangaren da kuma aiki tare domin amfanin duk wani ɗan Nijeriya. Nijeriya ce farko.”
Shelar da Shugaban ya yi ranar Alhamis ya zo ne kwanaki bayan Shugaba Tinubu ya yi kira ga masu ruwa da tsaki cewa rara da aka samu daga sauya ababen hawa zuwa masu amfani da CNG, ya kamata ya koma gun masu hawa ababen hawa ta raguwar kuɗin mota.
Daga farko dai ranar Alhamis, Ƙungiyar Gwamnoni ta goyi bayan tsarin arahar iskar gas ta CNG ta ƙasa domin rage kuɗaɗen ababen hawa da kuma rage tasirin cire tallafin mai kan ‘yan Nijeriya.
Gwamnoni sun sha alwashin taka rawar gani
Gwanonin sun ce tsarin, wanda ake tsarawa a matsayin tsari na matakin jiha tare da ɓangaren masu zaman kansu, zai yi amfani da ragin kuɗin gudanarwa na CNG domin rage tsadar kuɗin ababen hawa na sufurin jama’a.
Wannan matsayar ta fito cikin wata sanarwar ƙarshen taro da aka fitar bayan taron ƙungiyar gwamnonin na uku da aka fara a ranar Laraba da dare kuma aka ƙarƙare da safiyar ranar Alhamis a Abuja.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin wanda shi ne gwmanan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya rattaɓa hannu kan sanarwa kuma gwmnan jihar Bayelsa Douye Diri ya karanta shi bayan taron.
Gwamnonin sun ce tsarin zai ƙunshi tallafi na matakin jihar na sauya ababen hawa zuwa masu amfani da CNG da kuma samar da ababen more rayuwan masu alaƙa da kuma saka masu ruwa da tsaki a lamarin sufuri su ɗauki alƙawarin rage kuɗaɗen ababen hawa.
Ƙungiyar ta ce gwamnonin sun gane da cewa rage kuɗaɗen ababen hawa na da muhimmanci wajen rage tsadar rayuwa saboda ƙarin kuɗaɗen ababen hawa na tasiri kan kuɗaɗen kayayyaki.
“Sufuri na da muhimmanci. Sufuri na da muhimmanci game da wasu sauran dalilai ,” in ji gwamna Diri.
Ya bayyana cewa kuɗin tafiya da abinci da sauran ababe daga wani wuri zuwa wani wuri na bayyana cikin kuɗaɗen da masu amfani da abubuwa ke biya .
“Idan, alal misali, kana magana game da kayayyakin abinci—ƙarin farashin kayayyakin abinci, za su gaya maka cewa ina tafiya daga wuri na A zuwa wuri na B, kuɗin sufuri zai kai kaza.’ Kuma sabida haka, kuɗin doyana, kuɗin garri shi ne wannan ,” in ji Diri.
Matakin cire tallafin mai da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ɗauka a shekarar 2023 ya ƙara tsadar rayuwa a Nijeriya tare da ƙara wa jihohin ƙasar 36 ƙarin kuɗaɗen shiga.
Da aka tambaye shi game da iƙirarin da wasu ke yi cewa ba a san abin da jihohin ke yi da ƙarin kuɗaɗen da suke samu ba, Gwamna Diri ya ce wannan ba gaskiya ba ce domin gwamnoni za su iya bayani game da abin da suke da ƙarin ƙuɗaden da suke samu.





















