| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta gargaɗi al’ummomi 915 a jihohi 19 kan barazanar ambaliyar ruwa
Cibiyar Kula da Gargaɗin Ambaliyar Ruwa ta Kasa ta buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa su ɗauki matakan kariya cikin gaggawa tare da shirya yiwuwar kwashe su daga wuraren da ke cikin haɗarin.
Gwamnatin Nijeriya ta gargaɗi al’ummomi 915 a jihohi 19 kan barazanar ambaliyar ruwa
Yanayin ambaliyar ruwa a Nijeriya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi gargaɗi ga al’ummomi 915 da ke cikin jihohi 19 da Babban Birnin Tarayyar ƙasar Abuja kan babbar barazanar ambaliyar ruwa daga ranar 27 ga Agusta zuwa 9 ga Satumba.

Cibiyar Kula da Gargaɗin Ambaliyar Ruwa ta Kasa ta buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa su ɗauki matakan kariya cikin gaggawa tare da shirya yiwuwar kwashe su daga wuraren da ke cikin haɗarin.

Cibiyar ta sanya al’ummomi 915 cikin rukunin da ke cikin babban haɗarin ambaliya, waɗanda ke buƙatar sa ido da shirin ɗaukar matakan kariya.

An kuma sanya wasu al’ummomi 429 a jihohi bakwai cikin rukunin waɗanda ke cikin tsananin haɗari, yayin da wasu 656 a jihohi 13 ke cikin yanayin sa ido saboda yanayin matsakaicin haɗarin ambaliya.

Jihohin da ke cikin babban haɗarin sun haɗa da Kogi da Benue da Rivers da Edo da Delta da Cross River da Bayelsa da Akwa Ibom da Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da Imo da Ekiti da Legas da Ogun da Ondo da Osun da kuma Oyo.

Manyan birane da al’ummomin da aka ƙidaya a cikin rukunin barazanar ambaliyar ruwan sun haɗa da Lokoja da Makurdi da Port Harcourt da Benin City da Asaba da Calabar da Yenagoa da Uyo da Aba da Onitsha da Enugu da Owerri da Legas da Abeokuta da Akure da Osogbo da kuma Ibadan.

Gwamnatin ta ce yawan danshin kasa da yawan ruwan sama da ake samu da kwararar ruwa da kuma cunkoson magudanan ruwa da cikan koguna duk suna daga cikin abubuwan da ke ƙara barazanar ambaliyar.

A cikin sanarwar da Daraktan Sashen Kula da Zaizayar Kasa, Ambaliyar Ruwa da kuma Yankunan da ke Gabar Teku, Usman Abdullahi Bokani, ya sanya wa hannu, an bukaci mazauna yankunan da ke cikin haɗarin da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da tabbatar da hanyoyin da za su bi idan aka buƙaci kwashe su.

An kuma shawarci mazauna yankunan da su kula da mutanen da suka fi fuskantar barazana da kuma muhimman kayayyakinsu, tare da sai ido kan yanayin zamantakewarsu da kasuwanci da inda suke ajiye motoci da kuma yadda suke adana kayayyaki a wuraren da ruwa kan taru.

Gwamnati ta umarci hukumomin bayar da agajin gaggawa na jihohi da jami’an kula da muhalli da wakilan al’ummomi kan ambaliyar ruwa su kara sa ido kan wuraren koguna da bututun magudanan ruwa da gadoji da teku da madatsun ruwa da wuraren da ake samun zaizayar kasa.