An ji karar harbe-harben bindiga cikin dare a kusa da wani sansanin soji da ke filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa a Niamey, babban birnin Nijar, wanda ’yanta’adda suka kai wa hari sau biyu a bana.
Jama’a da dama a kafafen sada zumunta waɗanda ke zaune a Nijar sun kuma ruwaito cewa an ji harbe-harbe da fashe-fashe a cikin birnin, musamman a yankin gwamnati inda fadar shugaban ƙasa da gidan talabijin na ƙasa suke.
Wasu bidiyoyi da aka wallafa a intanet sun nuna motocin yaƙi masu sulke da aka jibge domin ƙarfafa tsaro a unguwar da ke kusa da filin jirgin saman.
A watan Janairu, ƙungiyar ta’addanci ta Deash da ke aiki a Sahel ce ta fara kai hari a filin jirgin, sannan a ƙarshen watan Yuni abokanan hamayyarta, ƙungiyar JNIM wadda ita ce reshen Al-Qaeda a yankin Sahel, suka sake kai wani hari.
Mahukunta sun ce a harin na watan Janairu, an kashe mahara 20 tare da jikkata sojoji huɗu.
A watan Yuni kuma, ma’aikatar tsaron ƙasar ta ce an kashe aƙalla sojoji 11 da fararen hula biyu, yayin da aka kashe maharan 22.
Rundunar sojin ƙasar ta daƙile duka hare-haren.

















