| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Boren soji a Yamai: AES ta jaddada goyon bayanta ga Nijar, ta yaba wa martanin dakarun tsaro
An shafe sa'o'i ana jin harbe-harbe masu ƙarfi cikin daren Asabar zuwa safiyar Lahadi a Yamai babban birnin ƙasar yayin da wasu sojoji suka yi boren da ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce dakarun gwamnati sun samu sun daƙile shi.
Boren soji a Yamai: AES ta jaddada goyon bayanta ga Nijar, ta yaba wa martanin dakarun tsaro
An kafa ƙungiyar AEs ne bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun fice daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka

Ƙungiyar Tarayyar Ƙasashen yankin Sahel (AES) ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga hukumomin Jamhuriyar Nijar ranar Asabar, biyo bayan boren da wasu sojoji suka yi a Yamai, inda ta yaba wa biyayya da jaruntaka na Dakarun Tsaron Nijar da ta ce su suka daƙile ƙoƙarin tayar da zaune tsayen.

Kamfanin dilancin labaran Jamhuriyar Nijar (ANP) ya ambato wata sanarwar da AES ta fitar ranar Asabar tana cewa tana tare da ƙasar wajen ci-gaba da “gwagwarmayar ‘yancin kai da zaman lafiya.”

“Saboda jaruntaka da ƙwarewa na dakarun jamhuriyar masu biyayya, an daƙile wannan sabon yunƙurin,” in ji sanarwar ta AES.

Kazalika ta yaba wa "biyayya da jaruntaka da tunani na aiki na dakarun tsaron Nijar, " waɗanda "suke biyayya ga rantsuwar da suka sha, suka fuskanci boren da kuma taka rawa wajen dawo da doka da oda ".

Ƙungiyar tarayyar ƙasashen ta kuma sake jaddada dagewarta wajen kiyaye "haɗin kai da zaman lafiyar yankin ƙungiyar tarayyar ƙasashen” inda ta yi kira ga mutane Burkina Faso da Mali da kuma Nijar su kasance masu sa ido sosai kan yaɗa labaran ƙarya da ƙoƙarin yamutsa tunanin mutane da kuma ƙoƙarin rarraba kawuna.