| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Babban Sufeton ‘Yansanda Nijeriya ya matsa kaimi don ceto waɗanda aka sace a masallacin jihar Neja
Babban sufeton ya bayyana cewa rundunar ‘yansanda ta tura ƙwararru kan yaƙi da ta’addanci da masu kawar da nakiya da masu aiki na musamman a wani ɓangare na ƙoƙarin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su da kuma dawo da tsaro a cikin gundumomin.
Babban Sufeton ‘Yansanda Nijeriya ya matsa kaimi don ceto waɗanda aka sace a masallacin jihar Neja
Babban Sufeton 'Yansandan Nijeriya, Tunji Disu / X/@PoliceNG

Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya bayyana ranar Asabar cewa rundunar ‘Yansandan Nijeriya tare da sauran hukumomin tsaron suna zafafa ƙoƙarinsu na ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke salla a massalaci a garin Dekara, ƙaramar Hukumar Borgu na jihar Neja.

Babban Sufeton ya bayyana wannan ne ranar Asabar a lokacin da ya kai ziyara ofishin rundunar ‘yansandan jihar Neja, inda ya yi ba’asi kan yanayin tsaro a jihar da kuma aikin da ake yi tare da ba da ƙarin tallafin kayan aiki ga rundunar.

Disu ya ce ya kai ziyarar ne da zummar ƙarfafa ƙoƙarin da ake na ceto masallatan da aka yi garkuwa da su, yayin da yake bayyana matakai a aikace da za su taimaka wajen warware matsalolin da jami’an tsaro ke fuskanta a jihar.

Ya yi Allah wadai da garkuwa da masallatan, yana mai tabbatar da cewa ƙasar ta damu matuƙa don gaggauta sakin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Babban sufeton ya bayyana cewa rundunar ‘yansanda ta tura ƙwararru kan yaƙi da ta’addanci da masu kawar da nakiya da masu aiki na musamman a wani ɓangare na ƙoƙarin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su da kuma dawo da tsaro a cikin gundumomin da lamarin ya shafa.

Ya ce hare-hare kan ‘yan ƙasa mara laifi na da tasiri sosai, ba kawai a kan tsaron mutane ba, har a kan harkokin tattalin arziki da ci-gaban jihar Neja da ma ƙasar baki ɗaya.

Disu ya yi kira ga jami’an rundunar ‘yansandan jihar Neja su ci gaba da sa ido sosai da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kuma jajircewa a kan ayyukansu.

Ya kuma yi kira ga rundunar ‘yansandan jihar ta ƙarfafa alaƙarta da al’ummomi da kuma tattara bayanan sirri, yana mai jaddada buƙatar da ke akwai ta tura bayanai masu tushe da za su iya hana kai hare-hare ga hukumomin da ya dace a tura wa.

Babban Sufeton ‘yansandan ya yaba wa jami’an rundunar bisa sadaukar da kansu da kuma ƙoƙarin da suke ci gaba da yi na kare rayuka da kadarori a faɗin jihar.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Neja, Adamu Elleman, ya bayyana jin daɗinsa ga tallafi da tabbacin da Babban Sufeton ‘Yansandan ya bai wa rundunar ‘yansandan jihar.

Babban Sufteon ya ziyarci gidan gwamnatin jihar inda mataimakin gwamnan jihar, Yakubu Garba, ya masa bayani game da yanayin tsaro a jihar.

‘Yanbindiga sun far ma gundumar Dekara ne ranar 22 ga watan Agustan shekarar 2026 inda suja yi garkuwa mutane da ba a san adadinsu ba bayan sun idar da sallar Jumma’a.

Sun kai harin ne tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa ƙarfe 2:30 na rana, in ji rahotanni.