| Hausa
SIYASA
3 minti karatu
Duk wanda ke alƙawarin dawo da tallafin mai yana yaudarar 'yan Nijeriya ne — Abdulaziz Yari
Yari ya ce babu tallafi a cikin kasafin kuɗin da majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi a shekarar 2023 kafin Shugaba Bola Tinubu ya karɓi ragamar mulkinn ƙasar.
Duk wanda ke alƙawarin dawo da tallafin mai yana yaudarar 'yan Nijeriya ne — Abdulaziz Yari
Toshon Hoto: Abdulaziz Yari shi ne Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen APC a zaben 2027

Sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Yamma kuma Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 ya ce duk wanda ke alƙawarin dawo da tallafin mai yana yaudara ‘yan Nijeriya ne.

Toshon gwamnan na jihar Zamfara, ya yi waɗannan kalaman ne ranar Asabar a lokacin da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar APC suka ziyarce shi.

Kalaman nasa martani ne ga alƙawarin da ɗan takaran shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027 Atiku Abubar ya yi cewa zai dawo da tallafin man idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen na 2027.

‘Dawo da tallafi ba zai yiwu ba’

Yari ya ce babu tallafi a cikin kasafin kuɗin da majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi a shekarar 2023 kafin Shugaba Bola Tinubu ya karɓi ragamar mulkinn ƙasar.

“Kafin Asiwaju ya shigo a shekarar 2023, ba a ware wa tallafi wani kuɗi ba a cikin kasafin kuɗi,” in ji Yari.

“Majalisar Dokoki ta amince da kasafin kuɗin a watan Maris ne, amma babu wani kuɗin da aka ware wa tallafin a kasafin kuɗin shekarar 2023. Ta yaya zai gudana? Lallai duk wanda yake wurin, abin da zai fara yi shi ne zai sallama,” in ji shi.

“Kuma duk wanda yake yaudarar ‘yan Nijeriya, yana cewa zan dawo da wannan abin, yana ƙarya ne wa kansa; yana ƙarya ta ciki, yana ƙarya ga ‘yan Nijeriya,” a cewarsa.

Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen APC ɗin ya yi tambaya game da kuɗin da aka kashe bisa tallafin a baya da kuma rashin bayani game iyan man da ake amfani da shi a cikin Nijeriya a ko wace rana.

“Wannan harka ce ta kimanin naira tiriliyan 20 a shekara, da ke tafiya inda ba mu sani ba. Babu wanda zai iya gaya maka, babu wanda zai iya gaya maka lita nawa muke buƙata, nawa muke buƙata a yini,” in ji shi.

Yari ya ce a lokacin da yake shugabancin ƙungiyar gwamnonin Nijeriya, gwamnonin sun yi ta ƙalubalantar kamfanin mai na ƙasa NNPC ya ba da cikakken bayanai game da iya man da Nijeriya ke sha.

“A matsayin shugaban ƙungiyar gwamnoni, mun ƙalubalanci NNPC na tsawon shekara huɗu ya gaya mana adadin man da muke sha,” in ji shi.

“Za su yaɗa adadin kuma su bayya shi, kuma muna biyan adadin. Daga baya da muka ƙara matsawa, suka ce a’a, ‘muna yi wa Afirka ta Yamma tallafi ne.’”

Yari ya ce APC za ta ɗaura yaƙin neman zaɓenta na shekarar 2027 ne kan nasarorin gwamnatin da shirye-shiryenta maimakon sukar ‘yan adawa ta siyasa.

“Muna kan hanya ta gaskiya. Da yardar Allah, muna da bayanan. Abin da za mu yi kenan a yaƙin neman zaɓenmu — sahihan bayanai da aƙalluma,” in ji shi.

“Abin da muka riga muka yi, abin da muka cim ma, kuma abin da muke son yi nan gaba. Ba ma kiran sunaye. Sunaye ba su da muhimmanci a gare mu, face abin da za mu yi wa ‘yan Nijeriya da kuma abin da muka kasance muna yi cikin shekaru uku da rabi da suka wuce,” in ji Yari.

“Bola Ahmed Tinubu yana iya ƙoƙarinsa, kuma mun yi imanin cewa shi ne ya fi dacewa da aikin,” a cewarsa.