| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
’Yan a-waren azbinawa sun saki sojojin Mali 60 da suka sace
Wata majiya mai tushe ta ce 'yan a-waren azbinawan sun saki sojojin ne a madadin ɗaya daga cikin shugabanninsu, Inkinane Ag Attaher, wanda aka kama a Nijar a shekarar 2025.
’Yan a-waren azbinawa sun saki sojojin Mali 60 da suka sace
Wata majiya ta biyu daga jami’an tsaro ta ce gwamnatin Nijar ce ta jagoranci yarjejeniyar musayar kai tsaye.

’Yan a-waren azbinawa sun saki kimanin sojojin Mali 60 domin musayar ɗaya daga cikin shugabanninsu da ake tsare da shi a maƙwabciyar ƙasar Nijar, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a ranar Jumma’a.

Majiyoyin, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce ƙungiyar azbinawan ta saki sojojin ne a madadin jami’inta, Inkinane Ag Attaher, wanda aka kama a Nijar a shekarar 2025.

Wata majiya mai tushe daga jami’an tsaron Mali ta shaida wa AFP cewa: “An kai kimanin sojoji 60 zuwa Nijar jiya domin musayar su da Inkinane Ag Attaher da wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da JNIM,” ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Qaeda.

Wata majiya ta biyu daga jami’an tsaro ta ce gwamnatin Nijar ce ta jagoranci yarjejeniyar musayar kai tsaye.

Mai magana da yawun kungiyar, Mohamed El Maouloud Ramadane, ya yi maraba da sakin Ag Attaher a wani saƙo da ya wallafa a Facebook, inda ya aike masa da saƙon fatan alheri.

Jami’an gwamnatin Nijar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan musayar ba, wadda ita ce sabuwar musayar da aka yi cikin jerin sakin fursunonin da aka kama a arewacin Mali a baya-bayan nan.

Ƙungiyar JNIM da ’yan tawayen azbinawan sun ƙaddamar da jerin hare-hare a cikin ’yan watannin nan kan muhimman wuraren da gwamnatin Mali ke iko da su.