| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Shugaba Tinubu zai tafi Turai don fara hutun makonni uku
Sanarwar ta ce ana tsammanin shugaban ya koma gida bayan "hutun aikin" domin shiga fafatukar yaƙin neman zaɓe na zaɓen watan Janairun shekarar 2027.
Shugaba Tinubu zai tafi Turai don fara hutun makonni uku
Toshon Hoto: A watan Mayun shekarar 2026 Shugaban Tinubu ya kai ziyarar aiki Birtaniya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai bar birnin Abuja zuwa Turai don fara hutun makonni uku a wani ɓangare na hutunsa na shekara-shekara.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi ta ce shugaban na Nijeriya zai ziyarci Landan a tafiyarsa a Turai ɗin.

“Ana tsammanin Shugaba Tinubu ya dawo gida bayan hutun aikin domin shiga fafatukar yaƙin neman zabe na zaben watan Janairun shekarar 2027,” in ji sanarwar Onanuga.