Sufeto-Janar na ’yansandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto-Janar na rundunar mai kula da shiyya ta 7, Victor Olaiya, zuwa jihar Neja domin jagorantar ƙoƙarin ceto masu ibadar da aka sace daga wani masallaci.
Rahotanni sun ce an sace mutanen ne a lokacin da suke gudanar da sallar Juma’a a wani masallaci da ke garin Dekara, a Karamar Hukumar Borgu ta jihar Neja, a ranar Juma’ar da ta gabata.
Matakin na zuwa ne yayin da hukumomi ke cewa har yanzu ba su tantance adadin mutanen da aka sace ba, kuma ‘yan bindigar ba su tuntube su ba.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar Neja, Obed Nuhu, ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da tattara bayanai kan lamarin, kuma har yanzu ba ta zanta da waɗanda suka kai harin ba.
Ya ce hukumomi na kokarin kauce wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano adadin waɗanda aka sace.
Kwamishinan ’yansandan jihar Neja, Adamu Elleman, ya ce an kuma tura rundunar yaƙi da ta’addanci da tawagogin binkice na musamman da kuma rundunar jiragen sama ta ’yansanda da sauran jami’an tsaro na musamman domin tallafa wa aikin ceto.
Ya ce jami’an tsaron na aiki tare da sauran hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Neja domin gano inda aka tafi da mutanen tare da kubutar da su.
Elleman, wanda kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya wakilta, ya ce jami’an tsaro na ƙoƙarin gano waɗanda suka yi garkuwa da Sarkin Guwa da kuma tsaurara ayyukan tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
A cewar Nuhu, hare-haren sun faru ne a wurare uku mabambanta a yankin, kuma ana zargin ƙungiyoyin Lakurawa da Boko Haram ne suka kai su.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya umarci hukumomin da abin ya shafa su hada kai da jami’an tsaro domin ceto mutanen da aka sace cikin koshin lafiya da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Gwamnatin jihar ta kuma ce dole jami’an tsaro su fara shawo kan batun matsalar tsaron al’ummomin da aka kai wa hare-haren baya-bayan nan kafin a kai tallafin jinƙai ga waɗanda abin ya shafa.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Maurice Magaji, ya ce gwamnati za ta tantance batun al’ummomin da lamarin ya shafa tare da samar da tallafin da ya dace da zarar jami’an tsaro sun tabbatar da samun cikakken iko a yankunan.





















