| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ghana ta kama mabarata fiye 1,000 a Accra da Kumasi – Hukumar Shige ta Fice ta Ghana
Aikin ya yi sanadin kama mutum 1,055, waɗanda suka haɗa da ƙananan yara 662 da mata 248 da kuma maza 145, a cewar Hukumar ta Shige da Fice ta Ghana.
Ghana ta kama mabarata fiye 1,000 a Accra da Kumasi – Hukumar Shige ta Fice ta Ghana
Waɗanda suka haɗa da ƙananan yara 662 da mata 248 da kuma maza 145, a cewar Hukumar ta Shige da Fice ta Ghana. / Facebook/Ghana Immigration Service

Hukumar Shige da Fice ta Ghana (GIS) ta kwashe mabarata daga ƙasashen Yammacin Afirka 1,055 daga kan titunan Accra da Kumasi a wani aiki da ta yi bisa bayanan sirri kan masu shirya bara da kuma ƙungiyoyin da ke kitsa safarar mutane.

Aikin wanda aka kammala a ranar Asabar, 29 ga watan Agusta, ya mayar da hankali ne kan ceto mutane masu rauni da kuma tarwatsa ƙungiyoyin da ake zargi da amfani da bara wajen safara da ci da gumin ‘yan ƙasashen waje musamman mata da ƙananan yara.

Aikin ya shafi wasu wurare da aka bayyana a matsayin inda lamarin ya fi aukuwa a Accra da Kumasi, inda jami’ai suka kama fiye da ‘yan Yammacin Afirka 1,000.

Hukumar ta GIS ta ce an kuma kama wasu ‘yan Ghana bisa zargin aiki a matsayin wakilai ga ƙungiyoyi masu ci da gumin mabaratan.

Aikin ya yi sanadin kama mutum 1,055, waɗanda suka haɗa da ƙananan yara 662 da mata 248 da kuma maza 145.

Hukumar ta salon aikinta mai dogaro ga bayanan sirri an yi shi ne domin ba kawai ɗon ɗabbaka dokokin shige da fice ba, amma domin gano tare da kuma kare mutanen da za su iya kasancewa waɗanda ake safararsu ko kuma ake musu sauran nau’o’i na ci da gumi.

A lardin Greater Accra, aikin ya mayar da hankali ne kan wasu wurare da aka gano cewa aka fi shirya yin bara a kan tituna.

Wuraren sun haɗa da Abossey Okai da Sabon Zongo da Madina Zongo Junction da  Madina da Ashaiman da kuma Tema.

A lardin Ashanti kuwa, jami’an GIS sun gudanar da aiki a yankunan Birnin Kumasi, ciki har da Asawase da Alabar da Akwatia Line da Dagomba Lin, da Sabon Zongo da Airport Junction da kuma Aboabo.

Hukumar ta ce an yi aikin ne a wuraren domin tarwatsa ƙungiyoyin da ke aika-aika a wurare daban-daban maimakon ɗauke masu bara kawai daga kan tituna.