| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Navone ya kare kokarin Djokovic don samun nasarar biyar a gasar US Open tun da ya fuskanci matsaloli da jiki a cikin zafi mai tsanani.
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Karon karshe da Djokovic ya yi rashin nasara a zagaye na farko na gasar Grand Slam shi ne a gasar Australian Open a shekarar 2006.

A karon farko cikin shekaru fiye da 20 an fitar da Novak Djokovic daga gasar US Open, daya cikin manyan gasannin tennis na duniya, tun a zagayen farko na gasar da ake yi a Amurka.

Ranar Lahadi ne gwarzon ɗan Tennis ɗin ɗan ƙasar Serbia, ya sha kashi ne a hannun Mariano Navone, ɗan Argentine, a wani yanayi da ake ganin Djokovic ya samu koma-bayar ne sakamakon jiyya da yake fama da ita, da kuma rashin lafiya.

Mai shekaru 39, Djokovic ya iso filin wasa na Flushing Meadows da ke New York da nufin samun kofi na biyar na gasar US Open, kuma na 25 cikin jerin manyan kofunan gasannin tennis.

"Wani abu ne da na daɗe ina ɗauke da shi, abin takaici, kusan a kowane wasa a bana. Amai, hararwa , babbar matsala ce. Sannan duk jikina ya fara sakwarkwacewa, kawai yana min ciwo da zogi.

“A ƙarshe dai gadon bayana da kafaɗu sun, har na gaza kammalawa. Shin za a iya gyara wannan matsala? Ban sani ba. Ina ƙoƙari, ina ƙoƙari. Bari mu gani."

Yanayin rauni

Lokacin da Djokovic ya sha kashi na ƙarshe a zagaye farko a babbar gasar tennis ta Grand Slam shi ne a Australian Open na 2006.

Djokovic ya shaida wa 'yan jarida cewa, "Gaskiya na ƙyamaci kowane minti da na kwashe a filin wasa saboda haka."

Duk da cewa babu Jannik Sinner, ɗanwasan Tennis na ɗaya a duniya a gasar, kuma babu zakaran gasar na bara, Carlos Alcaraz, Djokovic wanda ke zuwa bayan dogon hutun jiyya, ya shiga gasar da cikakken buri da damar lashe babban kofi na 25 a tarihin wasansa.

Amma abokin karawarsa, Navone ya samu gagarumar nasara a tarihin wasansa kan gwaninsa.

Da shi ma yake jawabi, Mariano Navone wanda ke matsayi na 49 a ƙwararrun ‘yanwasan tennis, ya ce, "Da yake samana da maki 0-3 da fari, na ji ɗan tsoro saboda girmamawa ga tauraron da nake fafatawa da shi.

“Ba sauƙi ba ne buga wasa da Novak, shi abin koyi ne. A gaskiya ya nuna rashin ƙarfin jiki a bugun ƙwallonsa, gaskiyar kenan."