| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Majalisar Dinkin Duniya ta amince a sake zana taswirar Afirka zuwa ainihin yadda nahiyar take
Togo ce ta jagoranci wannan yunƙuri domin ƙara ƙarfafa fafutikar Tarayyar Afirka ta rage amfani da taswirar Mercator, wadda ke gurbata bambancin girman yankunan ƙasa ta hanyar faɗaɗa wuraren da ke kusa da arewaci da kudancin duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta amince a sake zana taswirar Afirka zuwa ainihin yadda nahiyar take
Kudurin yana inganta amfani da taswirar Equal Earth, wadda ta fi nuna girman nahiyoyi yadda ya kamata.

Majalisar Dinkin Duniya a ranar Jumma’a ta kada ƙuri’ar amincewa da sauya taswirar duniya ta Mercator da aka ƙirƙira a ƙarni na 16, zuwa wata taswira da ta fi nuna ainihin girman ƙasashe yadda ya kamata. Ƙasashen Afirka ne suka ɗauki nauyin kudurin, domin magance ra’ayoyin da ke kallon nahiyar a matsayin wadda take a gefe.

Togo ce ta jagoranci wannan yunƙuri domin ƙara ƙarfafa fafutikar Tarayyar Afirka ta rage amfani da taswirar Mercator, wadda ke gurbata bambancin girman yankunan ƙasa ta hanyar faɗaɗa wuraren da ke kusa da arewaci da kudancin duniya. Taswirar tana nuna Greenland da girman da ya yi kusan daidai da Afirka, duk da cewa Afirka ta fi Greenland girma da kusan sau 14.

“Duniya mai adalci tana farawa ne da taswira mai adalci,” in ji Ministan Harkokin Wajen Togo, Robert Dussey, ga Reuters gabanin ƙuri’ar da aka kada a ranar Jumma’a.

Kudurin yana inganta amfani da taswirar Equal Earth, wadda ta fi nuna girman nahiyoyi yadda ya kamata.

Kudurin ba shi da ƙarfin doka, kuma “ba ya ƙalubalantar amfani da taswirar Mercator ta kowace hanya wajen zirga-zirgar jiragen ruwa da jiragen sama, waɗanda har yanzu taswirar ta dace da su sosai,” in ji ma’aikatar Togo a cikin wata sanarwa.

Amurka ta ƙi amincewa

An amince da kudurin a Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙuri’u 164 kan 1, yayin da ƙasashe 6 suka kaurace wa kada ƙuri’a.

Amurka, wadda ita ce ƙasa ɗaya tilo da ta kada ƙuri’ar adawa da kudurin, ta ce kudurin yana inganta “manufar akida” kuma yana kawar da hankali daga “ainihin matsalolin zaman lafiya na duniya, wadata ko kyakkyawar alaƙa.”

Dussey ya ce Togo za ta matsa wa sauran gwamnatoci, makarantu, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kamfanonin fasaha lamba su daina amfani da taswirar Mercator da aka kwashe ƙarnuka ana amfani da ita, yana ƙarawa da cewa taswirar Equal Earth tana ba da “mafi kyawun fahimta” game da duniya.

Dussey ya ce Togo na shirin ganawa da ƙasashe mambobin Tarayyar Afirka da masu mara musu baya daga wasu yankuna cikin watanni shida masu zuwa, domin cimma matsaya kan yadda za a ƙara yaɗa amfani da sabuwar taswirar.

Dussey ya ce tattaunawar kan matakan da za a ɗauka na gaba za ta buƙaci ta ƙunshi kamfanonin da ke gudanar da taswirori, GPS da sauran fasahohin da suka danganci gano wurare.

Dussey ya danganta kamfen ɗin na amincewa da sabuwar taswirar da ƙoƙarin da Afirka ke yi a faɗin nahiyar na tunkarar abubuwan da suka rage daga mulkin mallaka, yana mai cewa ba hari ba ne kan Turai ko wata wayewa.

Ya ce yawan amfani da taswirar Mercator a duniya sakamakon mulkin mallaka ne.

“Duniya tana sauyawa. Afirka ma tana sauyawa.”