Fiye da mutane 7,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), a cikin mummunar ɓarkewar cutar da aka taɓa samu a ƙasar, a cewar alkaluman da hukumomin Kongo suka fitar a ranar Asabar.
Sai dai gwamnatin ƙasar ta nuna cewa wataƙila yaɗuwar cutar ta riga ta kai kololuwa, duk da cewa an tabbatar da ɓullar cutar a lardi na bakwai a farkon wannan mako.
Kongo ta tabbatar da sabuwar ɓarkewar cutar a hukumance a tsakiyar watan Mayu, inda kusan mutane 3,400 suka mutu da wannan annoba ta 17 da cutar mai saurin yaɗuwa ta Ebola ta haddasa a ƙasar.
Barkewar ta fara ne a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin ƙasar, kafin ta yaɗu zuwa yankunan gabashi da arewa masu nisa, waɗanda rikice-rikice suka addaba, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai suka shafe shekaru da dama suna kai hare-hare, kasancewar ikon gwamnati ya yi rauni tare da ƙarancin cibiyoyin kiwon lafiya.
A farkon wannan mako ne aka tabbatar da cutar a lardin South-Ubangi, wanda ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Congo-Brazzaville.
A cewar sabbin alkaluman hukumomin Kongo, an samu jumullar mutane 7,022 da suka kamu da cutar tun bayan fara ɓarkewar. Daga cikinsu, mutane 3,398 sun mutu, yayin da 1,671 suka warke.
Mafi yawan waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar suna cikin Ituri, inda aka gano Ebola a wasu makarantu kwanaki bayan komawar ɗalibai makarantu bayan hutun bazara, lamarin da ya jefa iyaye da ma’aikatan kiwon lafiya cikin fargaba.
"Mun damu matuƙa saboda ba mu san wane yaro ya fito daga wane gida ba, ko kuma halin lafiyar mutanen wannan iyali," in ji Angele Magani, mahaifiyar wani ɗalibi a Bunia, babban birnin lardin Ituri a tattaunawarta da AFP.
"Mun tsorata sosai, duk da cewa hukumomin makarantar suna tabbatar mana da matakan kariya da aka ɗauka domin lafiyar yara," in ji ta.
Wani jami'in makaranta a Bunia, Roger Mungimbo, ya ce: "Akwai tsarin tilasta wanke hannu da sabulu, sannan mun yi duk mai yiwuwa domin kada adadin ɗalibai a aji ya wuce 30."
Ya ƙara da cewa, "Muna yawan wayar da kan yaran cewa ba su kamata su taɓa juna ba," tare da tunatar da su su rika wanke hannayensu akai-akai.
Ebola, wadda ta kashe fiye da mutane 15,000 a Afirka cikin shekaru 50 da suka gabata, tana yaɗuwa ne ta hanyar taɓa ruwan jikin wanda ya kamu da cutar, kuma tana iya haifar da mummunan zubar da jini a ciki da wajen jiki, tare da gaza aiki na sassan jiki.
Barkewar cutar ta yanzu ta samo asali ne daga nau'in kwayar cutar Ebola ta Bundibugyo, wadda babu wata allurar rigakafi ko magani da aka amince da shi a hukumance domin yakarta. Ana gudanar da gwaje-gwaje kan wasu magunguna da alluran rigakafi.
















