Fire da ‘yan ci-rani 1,000 ne aka ceto a cikin mako ɗaya kusa da tekun yammacin Afirka inda suka yi ƙoƙarin tafiya mai haɗari ta tekun Atalantika zuwa Turai, in ji ƙungiyar likitoci ta Doctors Without Borders (MSF).
Mutum 1,046 na tafiya ne a jerin kwale-kwale bakwai, waɗanda dukkansu sun tashi ne daga Gambia kuma suna kan hanyarsu ta zuwa tsibiran Canary Islands na Sifaniya, kafin su maƙale a teku, a cewar MSF a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Bayan an gano su a makon ƙarshe na watan Agusta, an kawo su Nouadhibou a Mauritania zuwa biarnen Rosso da Dakar a ƙasar Senegal.
Dubban mutane da akasarinsu matasa ne sun shafe shekaru suna ƙoƙarin bin hanyar tekun Atalantika mai hatsari kan kwale-kwale mara kyawu cike maƙil domin kia ga Turai ta tsibiran Canary Islands na Sifaniya.
Tserewa daga talauci
Da yawa na tserewa ne daga talauci inda suke zaɓi tafiya a kwale-kwale mara kyawu yayin da ƙasashen Turai ke tsabar taƙaita ba da biza da kuma ƙarfafa tsaro a kan iyakokinsu.
Waɗanda suka tsiran suna fama da wasu matsaloli, ciki har da matsananincin ƙarancin ruwa a jiki da ficewa daga hayyaci da targaɗe da tsananin gajiya da cututtuka na tumbi da fatan jiki da numfashi, a cewar MSF.
"Tasirin lamarin a kan tunanin waɗanda suka tsiran na da yawa, yayin da da yawa daga cikinsu suka ga yadda ‘yanuwansu suka rasu yayin ƙetarewar", in ji sanarwar.
A cikin masu ƙetarewar akwai mata 134, ciki har da ɗaya da take da ciki, tare da yara 88, in ji ƙungiyar.
Yawancinsu daga ƙasashen Senegal da Gambia, duk da cewa wasunsu sun fito ne daga Mali da Guinea Ivory Coast da wasu sauran ƙasashe.
Da yawa sun shaida wa MSF cewa an haɗa su da tashin hankali a ƙasashensu da hanyar zuwa ci-ranin.













