Barcelona, Real Madrid, da sauran manya-manyan ƙungiyoyin ƙwallo sun fara shirya yin wawason ‘yanwasan Manchester City ta Ingila, wadda ke fuskantar shari’a kan laifuka 115 da ake zargin ƙungiyar da aikatawa.
Zarge-zargen sun shafi keta dokokin hada-hadar kuɗaɗe, wadda ta sa City ke cikin barazanar rasa taurarin ‘yanwasanta kamar Erling Haaland na Norway, idan aka saka wa ƙungiyar takunkumi.
A watan nan ne aka samu City da laifuka 115, amma ba a kai ga yanke mata hukunci ba, kuma hukuncin zai iya shafar makomarta a tsawon shekaru masu zuwa.
Har yanzu ana kan turka-turkar shari’ar kuma hakan zai iya ɗaukar lokaci, saboda ana sa ran ɗaukaka ƙara daga Man City. Duk da haka ta kwan da sanin za ta iya rasa maki da yawa, wanda zai janyo a cire ta daga Gasar Firimiya.
Idan har hakan ta faru akwai yiwuwar taurarin ‘yanwasan ƙungiyar da dama za su ƙaurace mata don neman wasu kulob-kulob ɗin da ke buga manyan gasannin ƙasashe.
Baya ga Haaland, akwai manyan ‘yanwasa irin su Josko Gvardiol, Enzo Fernandez, Rayan Cherki, da Ayoub Bouaddi, waɗanda suke da masu zawarcinsu.
Sai dai kuma, yawancin ‘yanwasan suna da kwantiragi da Manchester City wadda ba za ta ƙare ba sai nan da shekaru. Misali, Erling Haaland yana da kwantiragi har shekarar 2034, kuma babu saɗarar da ta amince ya bar ƙungiyar idan ta faɗo daga Firimiya.
Irin wannan dalili ne ke sa masu sharhi ke ganin zai yi wahala City ta bar taurarin nata su guje mata, ko da ta faɗa ƙangin da take shirin afkawa.






















